Yadda direba ya kashe mai gidansa ma’aikacin CBN, ya kuma kashe matarsa da ɗansa

2
489

Waɗanda ake zargi da kashe tsohon ma’aikacin babban bankin Najeriya (CBN), Kehinde Fatinoye, da matarsa, Bukola Fatinoye da dansu ɗaya tilo a duniya Oreoluwa Fatinoye, sun bayyana dalilin da ya sa suka aikata wannan aika-aika.

‘Yan sanda sun gabatar da waɗanda ake zargin ne a ranar Juma’a a hedikwatar ‘yan sandan jihar Ogun, Eleweran, Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

A yayin faretin, jami’in hulɗa da jama’a na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa direban marigayin, Lekan Adekanbi, ya amsa cewa shi ne ya ɗauki nauyin sauran mutane biyu domin su taimaka masa wajen karɓar kuɗi daga hannun maigidansa.

Ya ce a lokacin da suke tare da waɗanda abin ya shafa, sun bukaci a ba su kuɗi, kuma waɗanda ake zargin sun san cewa za a iya bin diddigin su kuma suka yanke shawarar kashe ma’auratan domin su badda banin laifinsu.

KU KUMA KARANTA: Ya kashe mijin ƙanwarsa bisa zarginsa da bin mata

A cewar Oyeyemi, direban wanda a ranar 2 ga watan Janairu ya tsere daga hannun ‘yan sanda a lokacin da suka kai shi asibiti ana kula da lafiyarsa, bayan ya suma a hannunsu lokcin da suka kama shi, an gano ya tsere daga asibitin zuwa wajen ƙaninsa a garin Iseyin na jihar Oyo, amma kafin isowar ‘yan sandan ya kuma tserewa daga wajen.

Tawagar ‘yan sandan, kamar yadda Oyeyemi ya bayyana, sun ƙara zage dantse inda suka kama Adekanbi a maɓoyarsa a wani wuri a Abeokuta a ranar 21 ga watan Janairu.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, Adekanbi, wanda direba ne na waɗanda abin ya shafa tun daga shekarar 2018, “ya ​​furta cewa shi ne ya shirya wannan aika aika.

Oyeyemi ya ce: “Ya gayyaci sauran mutane biyun da ake zargin Ahmed Odetola (Aka akamo) da Waheed Adeniyi (Aka Koffi) domin su taya shi yi wa ma’auratan fashi.

“Ya kuma ƙara da cewa ya ɗauki matakin ne saboda ma’auratan sun ki ƙara masa albashi, kuma ya tuntuɓe su don neman rancen kuɗi ya sayi babur, amma suka ƙi ba shi rancen kuɗin.

“Ya shaida wa ’yan sanda cewa shi da ‘yan bindigar da ya ɗauka haya sun jira ma’auratan su dawo daga coci inda suka je hidimar sabuwar shekara ta Crossover Service, ya kuma ya sami shiga gidan ne kasancewar yana yiwa ma’auratan aiki, yana mai cewa sun kai musu farmaki nan take lokacin da ma’auratan suka dawo daga coci, inda bayan sun tursasa mutumin ya tura masu kuɗi sama da naira miliyan ɗaya da dubu 20 a asusunsu na banki, sai suka yanka wuyarsa da wuƙa suka kuma bugawa matarsa guduma itama ta mutu nan take, sannan da ɗansu da kuma ɗan da suke riƙo suka fito sai suka farmasu suka ɗaure su suka sanya su a mota suka jefa su cikin kogi, sai dai yayin da ɗan nasu aka gano gawarsa ɗan rikon ya tsira da ransa bayan da ya kwance igiyar da aka ɗaure masa hannu a cikin kogin” inji Abimbola Oyeyemi.

Ya ƙara da cewa karen ma’auratan da ke gidan bai kai wa direben farmaki ba, saboda karen ya saba da shi, domin shi ke ba shi abinci.

2 COMMENTS

Leave a Reply