Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba su da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa, ’yan gudun hijirar sun fito ne daga sassan jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato a yankin Arewa-maso-Yamma da jihohin Adamawa da Borno da Yobe a yankin Arewa-maso-Gabas.
A yanzu haka galibinsu sun faɗa barace-barace da kananan ayyuka ko sana’o’in da ba su taka kara sun karya ba, domin samun abin kai wa bakin salati.
Wasu daga cikin mabaratan da muka zanta da su, sun bayyana cewa, sun fito ne daga yankunan karkarar da matsalar tsaro ta yi wa dabaibayi a yankunan biyu.
A cewarsu, a baya sun kasance suna rayuwa cikin aminci da mutunci a yankunan nasu, inda suke kula da gonakinsu da dabbobinsu, sai dai bayan shafe shekaru ana tashe-tashe hankula na hare-haren ’yan fashin daji, lamarin da ya jefa su cikin baƙin talauci, inda mata da dama suka zama zawarawa, yayin da yara ƙanana suka koma marayu.
Lura da da cewa babu takamaiman sansanonin ’yan gudun hijira da gwamnati ta amince da su a wasu jihohin Arewa-maso-Yamman, wadanda ta’addancin ’yan fashin ya shafa, sun ce ba su da zabi illa su yi hijira zuwa wuraren masu tsaro kamar Abuja.
Sai dai jim kaɗan bayan sun samu mafaka a Abuja, galibinsu sun tsinci kansu tamkar a yanayin gudun gara a tarar da zago, yayin da suka fara fuskantar sababbin ƙalubale biyo bayan matakin da hukumar raya birnin Abuja ta ɗauka na kakkaɓe birnin daga gajiyayyu da mabarata.
Idan ba a manta ba, a watan Oktobar 2024 ne Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya umarci mabarata da su fice daga birnin ko kuma a kama su. Ministan ya yi tir da tururuwar mabarata da gajiyayyun, yana mai alakanta yawaitar gajiyayyun da ɓata-garin da ke sajewa ciklinsu, suna aikata miyagun laifuka da sunan barace-barace, wanda hakan a cewarsa ya sa aikin samar da tsaro a Abuja yake zama da wahala.
KU KUMA KARANTA:MƊD ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya samar da mafita ga ’yan gudun hijira
Wike ya ce, korar na daga cikin dabarun gwamnatin na dawo da martabar Abuja da kuma tabbatar da cewa birnin ya yi gogayya da sauran manyan biranen duniya.
Duk da cewa ’yan gudun hijirar sun bijire wa matakin, bisa dalilin cewa, bara ba ita ce rayuwar da suka zaɓa wa kansu ba, amma hukumomin Abujan sun yi kunnen uwar shegu da hanzarin mabaratan.
Rundunar haɗin gwiwa da ta kunshi ’yan sanda da sojoji da jami’an tsaron farin kaya da sauran jami’an tsaro ne suka gudanar da farmakin, inda a farkon farmakin sun yi kame a manyan wurare hudu: kwaryar birnin Abuja da hanyar zuwa tashar jiragen sama da yankin Kubwa zuwa Gwarinpa da kuma unguwannin Asokoro-Nyanya-Karu. Daga baya aka fadada shi zuwa sauran yankunan.
Kwamishinan ’yan sanda na Abuja, Olatunji Disu ya bayyana dakatarwar a matsayin “aikin kasa,” inda ya umurci jami’an da su aiwatar da aikin cikin himma da kwarewa.
Aminiya ta ruwaito cewa, bayan aikin da ya kakkaɓe su daga birnin Abujan, ’yan gudun hijirar sun koma wasu garuruwan Jihar Nasarawa, wadanda ke kusa da Abuja maimakon komawa jihohinsu.
Kodayake akan samu wasu mabaratan da suke sulalowa su shiga Abuja, suna bara da rana sannan su koma bayan gari zuwa yamma. Duk da haka, suna wasan buya da jami’an tsaro, inda hukumomin tsaron suke korar su daga kwaryar birnin Abuja da Kasuwar Wuse da Berger da unguwannin Utako da Jabi da sauran wurare a cikin birnin Abujan.