Yadda aka yi jana’izar Wazirin Borno, Mustapha Mukhtar

0
159

A ranar Asabar aka yi jana’izar Wazirin Borno, Yerima Mustapha Muktar, wanda Imam Idaini na Borno, Shettima Mamman Saleh ya jagoranta a Maiduguri.

Shugaba Tinubu ya yi juyayinsa rasuwar Wazirin Borno, a sakon taziyyarsa ga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya kuma roƙi Allah ya ƙisan sa ya ba wa iyalansa juriyar rashin.

Yerima Mustapha  wanda ya zama Wazirin Borno a 2007, shi ne firaminista kuma babban mashawarcin Shehun Borno; ya rasu yana d shekaru 50, ya bar mahaifiyarsa da mata huɗu da yaya, 19 da kuma ’yan uwansa.

KU KUMA KARANTA: Wazirin Fika, Malam Adamu Fika, ya rasu yana da shekaru casa’in

Dubban jama’a sun halarci jana’izar Wazirin Borno, ciki har da Gwamnan Babagana Zulum da mataimakinsa Umar Usman Kadafur da Sanata Kaka Shehu Lawan da Ministan Noma Abubakar Kyari da sauran jami’an gwamnati.

Shehu Dikwa, Ibrahim Ibn Umar Ibrahim, da Shehun Bama, Umar Ibn Shehu Kyari, da Sarakin Damaturu Shehu Hashimi II El-Kanemi da kuma Sarkin Gazargamu, Tijjani Ibn Saleh Gaidam, na cikin mahalarta jana’izar.

Ga yadda jana’izar kasance:

Leave a Reply