Yadda aka yasar da gawar sanatan Najeriya a Landan saboda talauci

0
269

An yi watsi da gawar marigayi sanata Joseph Wayas wanda shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya a jamhuriya ta biyu (1979-1983) a wani asibiti da ke Landan.

Wayas ya rasu ne a watan disambar 2021 a wani asibiti a Landan, sakamakon rashin lafiya da ya yi fama, wadda wasu ‘yan uwansa suka danganta da talauci.

Majiyar ‘yan uwa ta shaida wa jaridar Dailytrust cewa tallafin kudi ba ya zuwa gare su, kuma da kyar su ka iya jure wa. Gwamna Ben Ayade na Kuros Riba, inda marigayin ya fito, ya kaddamar da wani kwamitin jana’izarsa a watan Disamba 2021.

Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar ta baiwa kwamishiniyar lafiya ta lokacin, Dr Betta Edu da ta kula da harkokin lafiyar sa a Landan.

An ce gwamnatin jihar ta saki wasu kuɗaɗe ga kwamitin jana’izar karkashin jagorancin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Kanu Agabi sau biyu.

Sai dai bayan watanni 14 da rasuwarsa, bincike ya nuna cewa an yi watsi da gawar tsohon sanata a Najeriya wanda ya taɓa taka matsayin ɗan Najeriya mai darajar lamba ta uku kan wato shugaban majalisar Dattawa, kuma an yi watsi da gawar tasa ne a Landan akan rashin kuɗi.

KU KUMA KARANTA: Ranar Yara Ta 2022: Akasarinsu Yaran Najeriya Na Fuskantar Rayuwa Cikin Kunci Da Talauci – Inji Barista Ojukwu

Hakazalika sakamakon binciken ya nuna cewa a can ne aka samu cece-kuce a kan kuɗaɗen jana’izar da wasu manyan mambobin kwamitin suka yi murabus.

Ɗaya daga cikin manyan ‘yan kwamitin jana’izar tsohon babban sakataren hukumar tsare-tsare ta kasa, kuma mai fatan zama gwamna a wani lokaci, Ntufam Fidelis Ugbo, ya tabbatar da cewa tun a wancan lokaci ya fice daga kwamitin amma bai bayyana dalilansa ba.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan ya bayar da kuɗaɗe domin a binne marigayin amma ya ce dan na farko ga marigayin, Mista Joseph Wayas ƙarami, ya kamata ya kasance cikin yanayi mai kyau don bayyana dalilin da ya sa ba a gabatar da gawar mahaifinsa ba domin yi mata sutura.

“Ba zai iya cewa ba shi da wani bayani da zai bayar game da dalilin da ya sa aka jinkirta jana’izar, domin shine ɗan Marigayin na fari, ya kamata ya kasance mai kula”, inji Ugbo ya mayar da martani lokacin da aka faɗa masa cewa ɗan ya mika wakilin Dailytrust ga kwamitin.

Babban ɗa ga Marigayin, Wayas ƙarami, ya shaida wa Dailytrust cewa kwamitin jana’izar ne ke da nauyin gudanar da jana’izar, kuma ba shi da wani ta cewa, ya kuma yababwa gwamna Ayade bisa goyon bayan da ya baiwa kwamitin, amma ya ce watanni 14sun gagara binne mahaifinsa.

“Jana’izar ba a hannunmu take ba, amma yana rataye ne a wuyan kwamitin jana’izar, na ji akwai batutuwan da suka shafi kuɗaɗen jana’izar, kuma an ce wasu mambobin sun yi murabus daga kwamitin, ba zan iya komawa ga gwamnan jiha ko gwamnatin tarayya ba a yanzu saboda batun zaɓe” in ji shi.

A wata hira da aka yi da shi a baya, Wayas ƙarami ya yi nadamar jinkirin da aka samu wajen gudanar da jana’izar mahaifinsa, inda ya godewa shugaban kasa Muhamudu Buhari, wanda ya ɗauki nauyin tafiyar mahaifinsa zuwa Landan lokacin da ya fara jinya.

Ya ce mahaifinsa ya samu mafi kyawun kulawar jinya, amma kuɗin da ya bayar ya ƙare cikin watanni uku.

A cewarsa, kafin mahaifin nasu ya rasu, ‘yar uwarsa ce a Landan ce ta ɗauki nauyin jinyarsa, kuma tana kula da ɗawainiyar gawar tun shekarar 2021.

Da yake tsokaci, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dr Iwara Iwara, ya ce, “Kamar yadda aka sani, gwamnan jihar ya ƙaddamar da wani kwamiti. A matsayina na mutum, ban ƙara jin wani abu ba.

“Ba zan iya ba da dalilan da suka sa aka jinkirta jana’izar ba.”

Babban mashawarcin gwamnan kan harkokin yada labarai, Barista Christian Ita, ya ce, “Bana son shiga cikin lamarin. Wataƙila ɗan fari shine matsalar.

“Amma magana da membobin kwamitin jana’izar, a gaskiya gwamnan ya saki kudin jana’izar watannin da suka gabata.”In ji sa.

Leave a Reply