Yadda aka kashe jagoran ’yan ta’addan Katsina da yaransa

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe Maikusa, wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da ke jagorantar hare-hare a Jihar Katsina.

Maikusa ne mataimakin wani fitaccen ɗan ta’addan da ya addabi jama’ar Jihar Katsina Modi Modi, wanda ake nema ruwa a jallo.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Najeriya, Manjo-Janar, Onyema Nwachukwu ne ya sanar cewa sojojin sun hallaka Maikusa da wasu ’yan ta’adda uku ne a ranar Litinin, a tsakanin ƙananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar bayan bata kashin da sojin suka yi da ’yan ta’addan.

Ya ce, wannan gagarumin aiki ya yi nasarar kawar da ’yan ta’addar da suka jima suna addabar al’ummar yankunan.

A cewarsa, sojojin sun fuskanci turjiya daga ’yan ta’addar, amma dai sun yi galaba a kansu da ƙarfin wuta, inda suka hallaka su, yayin da wasu suka tsere.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a Borno, sun tarwatsa sansanonin su 25

Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji a cikin ’yan watannin da suka gabata sun kashe akalla manyan jagororin ’yan tada kayar baya bakwai a kasar.

Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Jaji ranar Talata.

Ministan wanda ya kai ziyarar aiki, ya a da jawabi ga sojojin da ke halartar wani taron kara wa juna sani da kwalejin yaki da ta’addanci da ’yan ta’adda.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *