Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023, ta kama wasu ‘yan ƙungiyar asiri guda biyar da suke tono gawarwaki daga cikin kabarinsu tare da cire wasu sassan jikinsu domin yin tsafi
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya ce waɗanda ake zargin; An kama sun haɗarda Oshole Fayemi mai shekaru 60, Osemi Adesanya mau shekaru 39, Ismaila Seidu mau shekaru 30, Oseni Oluwasegun mai shekaru 69 da Lawal Olaiya mau shekaru 50, an kuma kama su ne biyo bayan bayanai da rundunar ‘yan sanda ta samu a ofishinta na Odogbolu, cewa ‘yan ƙungiyar da ke da alhakin tono gawarwakin al’ummar Ososa suna shirin yin mummunan aikinsu na cire sassan jikin gawarwarkin da ke binne a kaburbura.
“Da samun labarin, DPO na Odogbolu, CSP Godwin Idehai, ya tattara mutanensa tare da kai farmaki maɓoyar waɗanda ake zargin inda aka cafke biyar daga cikinsu.
KU KUMA KARANTA: An gano gawar yaro ɗan shekara huɗu da ya ɓace a Abuja, an yanke sassan jikinsa
“A yayin da ake yi musu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun bayyana ikirari cewa a zahiri suna sana’ar tono gawarwaki ne daga kaburburansu, kuma sun kasance suna sayar da sassan jikin gawarwakin ga masu sayan su da ke bukata domin yin tsarin kuɗi”. In ji shi.
Yace a halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun CP Frank Mba, ya bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar domin gudanar da bincike na gaskiya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.