Ya mayar da Naira miliyan 4 da aka tura masa, a matsayin albashi
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rahotanni daga hukumar kwashe shara ta jihar Kano na cewa , ma’aikatan hukumar da sauran al’umma na ci gaba da yaba wa Mataimakin Shugaban hukumar Alhaji Lamin Muktar Hassan bayan ya mayar da kuɗi Naira miliyan 4 da dubu ɗari 7 da ɗoriya asusun gwamnatin Kano saboda tura masa a bisa kuskure.
Lamin bayan yaga, kudaden a zatonsa albashinsa ne na watan Janairun shekarar 2025 da aka fara biya ,sai kuma yaga kudaden sun zarce abinda yake dauka fiye da kaso 85 cikin dari na ainin albashinsa na wata wata.
Hassan Wanda gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada a matsayin mataimakin Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli ta REMASAB,ya dan samu tsaikun fara biyansa albashi a matsayinsa na DMD na hukumar tsawon wasu watanni,sai daga baya aka biyashi ariya dinsa gaba daya a watan Disamba na shekarar 2024.
A wannan watan na Janairu kuma aka sake turo min da irin kuɗaden da aka biyani na ariya a watan Disamba,wanda nasan kuskure akayi kuma a kudaden ma babu albashina na Janairu a ciki ,Inji Hassan.
A watan Maris na shekarar 2024 gwamna Yusuf ya nada Lamin Muktar Hassan a matsayin mataimakin Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano.
KU KUMA KARANTA:An karrama ɗan agajin da ya tsinci miliyan 100
Kafin nan Hassan shine yake rike Shugabancin hukumar kula da zurga zurgar jiragen sama ta Najeriya a jihar Gombe, wanda gwamna Yusuf ya nemi shi yazo ya bada gudun mowa a matsayin wucin gadi saboda kwarewarsa a bangaren abinda ya shafi tsaftar muhalli.
Mataimakin Shugaban hukumar ta kwashe shara a kano, wanda ya nemi a boye asalin abinda yake samu na albashi a duk wata, yace a yayinda yake jiran albashinsa na watan Janairu, sai yaga an turo masa kuɗi naira miliyan 4 da dubu dari 7 da doriya, sai ya garzaya ma’aikatar kuɗi da ofishin akanta domin sanar dasu halin da ake ciki.
Daga nan ma’aikacin sai ya tafi bankin da ake biyansa albashi na UBA ya mayar da kuɗaden gaba dayansu aka bashi shaida ya kai ma’aikatar kuɗin ta Kano.
DMD Lamin Muktar Hassan yace ya mayar da kuɗaden ne saboda yasan ba hakkinsa bane, kuma yayi hakan ne domin koyi da amanar da gwamna Yusuf na Kano yake da ita a karan kansa.
“A lokacin da na mayar da wadannan kuɗaden sama da naira miliyan 4 da dubu dari 7 bani da kuɗade kaso 10 cikin 100 a asusuna na abinda ya mayar din kuma, ban samu albashina na watan Janairun ba”Inji Hassan.
Yace a matsayinsa na mai kishin Kano da gwamnatin Kano ya zama wajibi ya mayar da kuɗaden domin a sallami wasu ma’aikatan koma ayiwa jama’a abinda ya dace da su.