Ya kamata a riƙa yin tsauraran hukunci kan maza masu dukan matansu – Sarkin Kano Sanusi II
Daga Jameel Lawan Yakasai
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci a ɗauki matakai masu tsauri kan maza masu aikata cin zarafin mata a jihar Kano, yana mai cewa babu musulmi nagari da ke dukan matarsa.
Ya koka kan yadda laifukan fyaɗe da na dukan mata daga mazajensu ke ƙara yawaita a jihar, yana mai cewa malamai da limamai na da rawar da za su taka wajen sauya ɗabi’un al’umma domin kawo ƙarshen wannan ɓarna.
Daily Trust ta rawaito cewa Sanusi ya yi wannan kiran ne a yau Litinin yayin da ya karɓi awagar cibiyar bincike da aiwatar da aiyukan ci bgaba (dRPC) da kuma Cibiyar Musulunci da Tattaunawar Addinai ta Jami’ar Bayero (CICID) a fadarsa da ke Kano.
A cewar Sarkin: “Ni ban yarda da dukan mace ba kuma wadanda suke yi ba don gyara suke yi ba. Abin da muke gani yanzu shi ne duka mai tsanani da jikkata mata da sunan gyara.
KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansandan Kano ta kafa kwamitin binciken rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado da Sarki Sanusi II
“Addinin Musulunci ya girmama mata fiye da kowanne addini, kuma duk wanda ke fakewa da addini domin cin zarafi ko dukan mace, bai fahimci addinin ba.
“Duk wanda ke dukan matarsa har ya jikkata ta, ba mutum nagari ba ne. Ni ban fada ba, Annabi Muhammadu (SAW) ne ya fada. Masu karatu ne kadai za su fahimta,” in ji Sarkin.









