Wike ya ƙira taron gaggawa kan matsalar tsaro a Abuja

0
135

Daga Maryam Umar Abdullahi

Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ƙira taron gaggawa na majalisar tsaro a sakamakon taɓarɓarewar tsaro a Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙira taron gaggawa na majalisar tsaro a sakamakon taɓarɓarewar sha’anin tsaro a sassan babban birnin.

Zaman nasa da shugabannin hukumomin tsaro da shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya na gudana a halin yanzu.

Gabanin fara zaman, ministan ya buƙaci hukumomin tsaro da su sabunta dabarun aikinsu domin daƙile duk wata barazanar tsaro da kuma tabbatar da aminci a faɗin Abuja.

Leave a Reply