WHO ta taimaka wajen kwashe marasa lafiya 14 daga Asibitin Nasser da ke Gaza da aka yi wa ƙawanya

0
174

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta taimaka wajen kwashe majinyata 14 daga Asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza, wanda sojojin Isra’ila ke yi wa ƙawanya, in ji Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kai marasa lafiyan, wadanda suka hada da biyar da aka yi wa wankin ƙoda da uku da ke cikin tsananin kulawa, zuwa asibitocin da ke kudancin kasar, sakamakon ƙoƙarin da hukumar ta WHO ta yi.

KU KUMA KARANTA: Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta shirya da Isra’ila ba, sai ta tsagaita wuta a Gaza

Ta ce ana ci gaba da matsa lamba kan Isra’ila ta kwashe dukkan majinyata daga asibitin, wanda ta mayar da shi barikin soji bayan katse wutar lantarki da kuma hana na’urorin iskar oxygen aiki.

Leave a Reply