Waye ya kashe tsohon shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa David Shikfu Parradang?

0
7
Waye ya kashe tsohon shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa David Shikfu Parradang?

Waye ya kashe tsohon shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa David Shikfu Parradang?

Daga Idris Umar, Zariya

Mai maganar da yawun ƴansandan Josephine Adeh tace tsohon jami’in ya mutu ne a wani otel da ake kira Joy House, dake unguwar Area 3 a cikin Abuja.

Mai magana da yawun rundunar ta ce da misalin karfe 12 rana a jiya Litinin, Parradang ya je otel din a cikin wata bakar mota kirar Mercedes, ya kuma kama daki bayan ya biya naira 22,000, yayin da daga bisani ya bai wa jami’an dake kula da otel ɗin umarnin su raka wata mata inda yake a cikin ɗakin.

Adeh ta ce da misalin karfe 4 na yamma, matar ta fice daga ɗakin, yayin da shi kuma tsohon jami’in ya ci gaba da zama a ciki ba tare da jin ɗuriyar sa ba.

KU KUMA KARANTA:A gaggauta biyan Malam Bature Jibrin haƙƙoƙinsa – Gwamna Uba Sani

Ƴansandan sun ce da misalin karfe 4 na asubahin yau Talata, wani abokinsa da ya gabatar da kansa a matsayin jami’in soji, ya ziyarci otel ɗin saboda damuwa da rashin jin ɗuriyar Parradang, amma da suka je ɗakin da yake tare da ma’aikacin otel ɗin sai suka same shi zaune a kujera amma babu rai.

Adeh tace nan take aka sanar da ofishin su dake Durumi, inda jami’ansu suka ƙaddamar da bincike, yayin da aka kai gawarsa asibitin ƙasa dake Abuja.

Leave a Reply