Wata mata ta yi nasara a kotu kan ƙin saduwa da mijinta

0
363
Wata mata ta yi nasara a kotu kan ƙin saduwa da mijinta

Wata mata ta yi nasara a kotu kan ƙin saduwa da mijinta

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata mata a Faransa wadda ta daina amincewa da mijinta ta samu nasara a wata shari’a da aka tafka a kotun kare hakkin bil’adama ta nahiyar Turai.

Matar, wadda aka kira ta da suna H.W, wadda ke zama a wani gari da ke kusa da birnin Paris na ƙasar Faransa, ta auri mijinta mai suna JC ne a shekarar 1984.

Sun haifi ƴaƴa huɗu, ciki har da wata yarinya mai lalurar da ke neman kulawa a koda yaushe.

Auren nasu ya fara samun matsala ne a shekara ta 1992 lokacin da matar ta fara samun lalura.

Bayan shekara biyu, H.W ta daina kwanciyar aure da mijin nata, sannan a shekarar 2012 ta shigar da buƙatar neman raba auren, bayan mijin ya fara tsangwama da ‘cin zarafinta’.

A ranar Alhamis, kotun da ta yanke hukunci ta goyi bayan H.W, inda ta kafa hujja da cewa bai kamata a zargi matar da aikata wani laifi ba saboda kawai ta ƙi amincewa da mijin nata.

Shari’ar ta haifar da zazzafar muhawara kan ƴancin mata a cikin gidajen aure a Faransa.

Leave a Reply