Wata mata a Kaduna ta nemi a raba aurenta saboda shirin mijinta na sayar da gidansu

Wata matar aure mai suna Sadiya Bashir ta nemi a raba aurenta a wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa a jihar Kaduna kan shirin mijinta na sayar da gidansu da kuma auren wata mata.

Mai shigar da ƙarar ta shaida wa kotu cewa mijinta, Abdullahi Haruna ba ya ba ta abinci da ‘ya’yanta 10, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Sai dai Haruna ya tabbatar da cewa yana son ya auri wata mata amma ba shi da niyyar siyar da gidan.

Ya ce ya kasance yana ciyar da iyalinsa bisa iyawarsa, inda ya bayyana cewa yana zaune lafiya da matarsa, har sai da shirinsa na auren wata ya zo mata.

Alkalin kotun, Muhktar Mu’azu ya umarci ma’auratan da su gabatar da shaidunsu a gaban kotu a ranar 14 ga Nuwamba, 2023.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *