Wata kotu ta yanke wa wasu ma’aurata hukuncin rataya

0
60
Wata kotu ta yanke wa wasu ma'aurata hukuncin rataya

Wata kotu ta yanke wa wasu ma’aurata hukuncin rataya

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Jihar Jigawa ta yanke wa wani miji da mata, da wasu ’yan uwanta biyu, namiji da mace hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Birnin Kudu ne ya yanke hukuncin bayan ya samu waɗanda ake tuhumar da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu Musa mai shekara 30 bayan sun yi zarginta da maita.

Kotun ta yanke hukuncin a wannan Larabar, 4 ga watan Disamba a shari’ar da aka shafe tsawon lokaci tun bayan kama waɗanda lamarin ya shafa a shekarar 2019.

Bayanai sun ce waɗanda aka yanke wa hukuncin waɗanda mazaunan garin Kwan-Dole na Ƙaramar Hukumar Malam Madori sun lakaɗa wa Salamatu duka da itace bayan sun yi zargin ta lashe musu ɗansu.

KU KUMA KARANTA: Wani magidanci ya karya ƙafa da hannun matarsa saboda fita ba da izininsa ba

Hukuncin wanda Mai Shari’a Birnin Kudu ya ce yana da madogara a sassa na 97 da 221 (7) na Kundin Dokokin Laifuka, ya ce waɗanda abun ya shafa suna da kwanaki 90 su ɗaukaka ƙara.

Leave a Reply