Wata kotu a Kano ta tura masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali

0
74
Wata kotu a Kano ta tura masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali

Wata kotu a Kano ta tura masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali

Wata kotun tafi-da-gidanka ta Jihar Kano ta ba da umarnin aika masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali bisa tuhumarsu da sace-sace da ɓarnata kayayyakin al’umma da na gwamnati a ranar farko ta zanga-zangar da aka yi.

Ana tuhumar mutanen da laifuka bakwai da suka hada da kitsa aikata mugayen laifuka da sace-sace da taruwa ba bisa doka ba da tunzura tashin hankali da shiga wurare ba tare da izini ba da kuma tayar da wuta.

Alƙalan kotunan sun bayar da umarnin tsare waɗanda ake tuhumar a gidan gyaran hali tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Agusta, 2024.

Tun da fari babban mai shigar da ƙarar na ma’aikatar shari’a Salisu Tahir ya yi zargin cewa mutanen sun aikata laifukan ne a ranar 1 ga watan Agusta inda suka kutsa tare da ɓaranata kayayyakin gwamnati da na al’umma a jihar.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu ɗaga tutar ƙasar Rasha

Wasu waɗanda ake tuhumar sun amsa laifukansu yayin da sauran suka musanta tuhume-tuhumen.

Atoni Janar na Jihar Haruna Isa-Dederi ya ce gwamnati ta samar da kotunan tafi-da-gidanka har uku don gurfanar da waɗanda ake zargin, kuma za a yi nazarin shari’ar kafin zama na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here