Wasu Sojoji sun koka kan rashin biyan su alawus ɗin ayyukan su

0
37
Wasu Sojoji sun koka kan rashin biyan su alawus ɗin ayyukan su

Wasu Sojoji sun koka kan rashin biyan su alawus ɗin ayyukan su

Wasu daga cikin sojoji da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Zamfara sun koka game da yawan jinkirin da ake samu, wajen biyansu kuɗaɗensu na alawus, inda suka ce akan biya su kuɗin wata guda ne kacal bayan kwashe watanni biyu ko uku, lamarin da ke jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a cewarsu.

Sai dai hukumomin sojan Najeriyar sun ce suna sane da wannan ƙalubale da ke gaban dakarun da ke fagen daga, amma ana ƙoƙarin shawo kan lamarin nan ba da daɗewa ba.Wasu sojojin da suke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji a jihar ta Zamfara, ne suka shaida wa BBC ƙorafin nasu.

KU KUMA KARANTA:Sojoji a Taraba sun kama masu garkuwa da mutane 10

Sun bayar da misali da cewa, sai a ranar Litinin ta wannan mako aka fara biyansu alawus na watan Mayun da ya gabata.

Har ma sun fara bayyana fargaba, cewa mai yiwuwa kafin a biya su alawus na watan Yuni sai cikin watan Satumba mai zuwa.

Sun ce akwai ma waɗanda daga cikinsu har yanzu ba a ma biya su alawus na watan Maris ba.

Sojojin da ke fagen dagar suna bara, cewa tsaikon biyansu alawus na jefa su cikin tsaka-mai-wuya.

Dangane da waɗannan korafe-korafe dai, BBC ta tuntubi Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar, mataimakin daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, inda ya yaba da irin ƙoƙarin da dukkan jami’ansu suke yi wajen yaki da ƴan’ta’adda.

Sannan ya ce: “Shugaban sojoji Janar Christopher Musa, zai yi duk abin da zai yuwu domin ganin an kyautata masu, kuma su ci gaba da samun nasarori a daƙile ƴan ta’adda, dangane da matsaloli da ake fuskanta, ana kan yin abin da ya dace, da zaran babban bankin Najeriya ya kammala aikinsa kowa zai samu abinshi, Insha Allah.”

Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar ya ce Janar Christopher Musa ya yi kwamandan yaƙi saboda haka ya san dukkan matsalolin da ke tattare da soja a daji, “Kowa zai samu kuɗinsa kai tsaye ta asusun bankinsa saboda haka ake yi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here