Wasu matasa a Bauchi sun ƙone ɓarayin adaidaita sahu har lahira
Wasu fusatattun matasa sun ƙone wasu mutum biyu har lahira, bayan an zarge su da kashe wani matuƙin adaidaita sahu tare da sace babur ɗinsa a Ƙaramar Hukumar Misau a jihar Bauchi.
Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kisan wani matashi mai shekara 25, Muhammad Mamuda Baba Jibir.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Wakil ya ce, “Eh, an samu laifukan haɗin baki, fashi da makami, da kuma kisan kai.
A ranar 18 ga watan Agusta, 2024, da misalin ƙarfe 10 na dare, ‘yan sandan Misau sun samu rahoton daga wani bawan Allah wanda ya ga wata gawa cikin jini a Anguwan Agwaluma, a wajen garin Misau.”
KU KUMA KARANTA: Wani ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi
Wakil ya ƙara da cewa, “Lokacin da ‘yan sanda suka isa wajen, sun tarar an yanka wuyan mutumib da wuƙa. An tabbatar da rasuwar wanda aka kashe mai suna Muhammad Mamuda Baba Jibir daga Sabon Layi, garin Misau, a asibiti a Misau.
“Masu laifin sun sace babur ɗin wanda mutumin ƙirar boxer. An miƙa gawar ga iyalansa don yi masa jana’iza.
“A ranar Litinin ’yan sanda sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da sace babur ɗin a kan hanyar Misau-Kari.
Amma kafin su isa ofishin ‘yan sanda, wasu gungun mutane suka kai farmake tare da ƙone su har lahira. An ƙone ɗaya daga cikinsu har sai sa ya zama toka, amma an ƙwato babur ɗin,” in ji Wakil.
Kakakin ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Auwal Musa Mohammed, ya yi Allah-wadai da yadda mutane suka ɗauki doka a hannunsu.