Wasu iyaye sun kashe ɗansu saboda gudun nan gaba ɗan zai koma ga Aljani

A kwanakin baya ne kafar yaɗa labarai ta BBC ta kama wasu fitattun ma’auratan Tiktok, Godpapa The Greatest da Empress Lupita a Ghana bisa zargin kashe ɗan nasu.

Da aka yi hira da mahaifiyar, ta bayyana cewa ita tare da mijinta sun kashe ɗan nasu ne saboda sun ga nan gaba zai koma ga Aljani ya ƙara haifar da Aljanu da za su halaka ƙasarsu ta Ghana.

A cewarta, sun kashe yaron ne a matsayin hanyar sadaukar da shi domin ƙasar Ghana don kada ƙasar ta lalace a hannunsa.

Ta ci gaba da cewa sun yi imanin cewa wannan yaron yana da aljani kuma idan ya girma zai riƙa aikata miyagun ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Abun sha’awa: Yaro mai fuskar al’ajabi da shuɗin launin idanu

Ta ce, ni da mijina ne muka kashe ɗanmu saboda mun ga nan gaba zai koma Aljani, mun kuma ga idan ya girma zai haifi wasu aljanu da za su halaka Ghana. “Mun sadaukar da shi ne domin ƙasar”.


Comments

One response to “Wasu iyaye sun kashe ɗansu saboda gudun nan gaba ɗan zai koma ga Aljani”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Wasu iyaye sun kashe ɗansu saboda gudun nan gaba ɗan zai koma ga Aljani […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *