Wasu fusatattun matasa a Kano sun kwashe shinkafa a gidan wani jami’in gwamnati
Daga Shafaatu Dauda, Kano
Rahotanni daga unguwar Gandun albasa da ke ƙaramar hukumar birni a jihar kano, ta tabbatar da cewa wasu matasa sun farwa wata makaranta mai suna Wada Sagagi, inda suka kwashi shinkafa mai rubutun gwamnatin tarayya a jikin buhunta.
Wasu mazauna unguwar sun ce, matasan sun shiga gidan ne da talatainin daddare, domin kwasar shinkafar da ake zargin wadda gwamnatin tarayya ta aiko ne domin rabawa mabukata a jihar.
Makarantar dai, na zaune ne a tsohon gidan shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kano, Alh Shehu Wada Sagagi.
Duk ƙoƙarin da wakiliyar Neptune Prime Hausa ta yi domin jin ta bakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Shehu Wada Sagagi da zargin ke alakantawa da kayan, lamarin yaci tura.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Kano ta kama ƙasurgumin ɗan fashi da makami
Amma shugaban makarantar Islamiyyar ta Wada Sagagi, ya tabbatar da faruwar shigar matasan cikin makarantar tare da kwasar buhunhunan shinkafar.
Idan za a iya tunawa makwani biyu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta ce ta turawa gwamnonin jihohin Najeriya tirela 20 ta Shinkafa zuwa kowacce jiha domin rabawa talakawa don magance matsalolin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya.