Wasu ɓatagari a Kano, sun tursasa wa mata mai ciki har ta haihu, sun gudu da jaririn

0
29
Wasu ɓatagari a Kano, sun tursasa wa mata mai ciki har ta haihu, sun gudu da jaririn

Wasu ɓatagari a Kano, sun tursasa wa mata mai ciki har ta haihu, sun gudu da jaririn

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wani mummunan lamari da ya girgiza al’umma ya faru a jihar Kano, inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka sace wata mata mai juna biyu, suka tilasta mata haihuwa, sannan suka tsere da jaririnta.

Rahotanni sun nuna cewa matar mai juna biyu ta kai wata tara na ciki tana kan hanyarta ta komawa gida ne, lokacin da batagarin suka tareta suka kuma yi awon gaba da ita zuwa wani wuri da ba ta iya gane inda ne ba.

A cewar matar, bayan an kai ta wannan wurin, wani mutum da ya bayyana a matsayin jami’in lafiya ya ba ta wasu kwayoyi, wanda hakan ya haddasa nakuda. Sai ga haihuwa nan take. Daga bisani, suka shaida mata cewa jaririn kawai suke bukata, don haka ba za su cutar da ita ba.

KU KUMA KARANTA:Muna ganin ribar ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

Wasu mazauna unguwar sun bayyana cewa tun kafin aukuwar lamarin, matar ta sha yawan korafi cewa tana jin kamar ana binta ko kuma ana saka mata ido.

Mijin matar ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki, inda hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin al’umma, inda ake kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa wajen kare rayuwar mata da lafiyarsu, da kuma tabbatar da adalci ga iyalan da abin ya shafa.

Leave a Reply