Danakil Depression, wani yanki ne mai ban sha’awa a Arewacin Lardin Afar da ke ƙasar Habasha (Ethiopia). Ana yi masa laƙabi da wuri ‘mafi zafi a duniya’ kuma ya na da tafkuna masu ruwan gishiri da duwatsu masu aman wuta.
Danakil, sarari ne mai faɗin murabba’i 200, kilomita 50 (124 ta 31 mi), ya na kwance a arewacin yankin Afar na Habasha, wadda ke kusa da kan iyaka da ƙasar Eritrea.
Bugu da ƙari, ya na da kimanin tsayin mita 125 (410 ft) watau ƙasa da matakin teku, kuma ya na iyaka da yamma da tsunukan Habasha sannan daga gabas da tsaunukan Danakil, bayan haka akwai Bahar Maliya.
Har ila yau, masu yawon buɗe ido na ziyartar wurin daga sassa daban-daban na duniya.
📷 The Atlantic