Wani uba da aka kashe ɗansa na neman adalci, ya koka kan diyyar naira dubu 600 da aka ba shi

0
399

Danjuma, mahaifin Mohammed Danjuma da aka kashe, ya koka yana neman a yi masa adalci, kan kisan gillar da aka yi wa ɗansa.

An yi zargin kashe Mohammed mai shekaru 34, wanda ya kammala karatun digiri na biyu a makarantar horar da ma’aikatan jiragen ruwa ta Nigerian Maritime Academy da ke Oron, a ranar 7 ga watan Yulin 2022, a unguwar da ke titin Clapperton, a jihar Sakkwato.

Mahaifin marigayin, Danjuma Sidi, wanda ya ba da labarin irin halin da ‘yan uwa ke ciki, ya bayyana wa manema labarai cewa, ana zargin ana shirin yin maƙarƙashiya da bincike inda ya gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da kisan dansa.

Ya ce rundunar ‘yan sandan Sakkwato ba ta bada wani taimako da tayi masu, domin duk ƙoƙarin da suka yi na neman ‘yan sanda game da kisan da ake zargin, hukumar ta PPRO ta yi watsi da su.

KU KUMA KARANTA:Wani matashi da ya kashe budurwarsa don ya saci motarta ya shiga hannu

Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar a ranar larabar da ta gabata, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Abubakar Sanusi, ya yi wa ‘yan jarida alkawarin za su binciki lamarin tare da yi musu bayani.

Cike da hawaye, Ɗanjuma Sidi ,ɗan shekaru sittin da biyu, ya shaidawa manema labarai cewa an kashe Mohammed, a ranar 7 ga Yulin 2022, kuma bayan watanni biyar, waɗanda ake zargin da kashe shi, suna kan titi suna yawo cikin walwala.

“Akwai shaidar bidiyon da ke yawo, inda aka ɗaure ɗana, aka azabtar da shi, aka wulakanta shi,har ya mutu. Daga nan ne ‘yan sanda suka kai farmaki inda aka kama mutane shida.

“A dalilin binciken, dangin waɗanda ake zargin sun tuntuɓe mu, tare da rokon a sasanta lamarin ba tare da an kai ga ‘yan sanda ba. Na ce da su su ƙyale a yi adalci domin babu wani sassan ta da zai dawo min da ɗana. Sun tafi sun yi alƙawarin dawowa gareni.

“Abin takaici, suka dawo bayan sun saba alƙawarin haɗuwar mu har sau biyu, suka ba ni naira dubu ɗari shida kacal, a matsayin diyya na ran ɗana, tare da binne lamarin.

” Wannan, na ƙi karba, domin idan za su ba ni diyya a Musulunci, ba wannan dan ƙaramin kuɗi naira dubu ɗari shida zasu bani ba.

“Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da ta tarayya, da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, da ƙungiyoyin kare hakkokin ɗan Adam da ‘yan jarida, da su taimaka wajen ganin an yi adalci ga ran ɗana da aka kashe”. Inji shi.

Leave a Reply