Wani mutum ya lakaɗa wa budurwarsa duka ta mutu har lahira a Kuros Riba

Rundunar ‘yan sanda a Kuros Riba da ke Kudu-maso-Kudu ta Najeriya ta kama wani mutum mai shekaru 54 bisa zarginsa da lakaɗa wa budurwarsa duka, ta mutu har Lahira a ƙaramar hukumar Kalaba ta Kudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta tabbatar da kamun a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kalaba ranar Laraba.

Ta ce wanda ake zargin mai suna Ndifreke ya yi mata dukan ne, bayan wata ‘yar ƙaramar rashin jituwa da ta faru a titin Abasi Obori ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: Ɗan fari ya kashe ɗan autansu da duka, ya raba kansa gida biyu

Misis Ugbo, Sufeto na ‘yan sanda, ta ce jami’an ‘yan sanda daga Hedikwatar ‘yan sanda ta Uwanse ne suka gudanar da kama a lokacin da suka isa wurin bayan wani ƙiran gaggawa da aka musu.

“’Yan sanda sun garzaya da wanda aka yiwa duka zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Calabar. Abin takaici, ba a ƙarasa ba ta rasu, saboda an tabbatar da cewa ta mutu a isowar likitan da ke bakin aiki.

“Bayan ƙa’idojin da aka kafa, an ajiye gawarta a ɗakin ajiyar gawarwaki domin a tantance gawarta ta, domin yin ƙarin haske kan ainihin musabbabin mutuwarta.

“Tuni wanda ake zargin yana hannunmu kuma za mu tabbatar da cewa ya fuskanci cikakken hukunci kan laifin da ake zarginsa da shi,” in ji kakakin ‘yan sandan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *