Wannan mutumi ya kashe zaki a gabashin Afirka, inda ya samu raunuka da dama bayan ya yi faɗa da zakin na tsawon mintuna 90 don kare iyalansa.
Hotunan dake da ban tsoro sun fito daga ƙasar Uganda bayan da rahotanni suka ce wani mutum ya kashe zaki da hannunsa a wasan kokawa da aka yi wanda yai sanadin zubar jini mai yawa daga jikin mutumin wanda za ku ga duk jikinsa ɗaure da bandeji.
Shafin Daily Star ta rawaito cewa mazauna yankin da mutumin ya fito sun tabbatar da faruwar al’amarin inda suka ce zakin ya yi ƙoƙarin shiga gidan mutumin inda suka fara yin kokawa da mutumin.
KU KUMA KARANTA: Habasha, tsarin kalandar su, da sauran al’adunsu na ban mamaki
An ɗauki hoton mutumin cike da raunuka a jikinsa duk an yi masa liƙi da bandeji kamar yadda kuke gani cikin wannan hoton wanda zai iya ɗaukar tsawon lokaci kafin ya warke.
Mutane da yawa ne ke ta ce-ce-ku-ce a kan yadda mutumin ya nuna jarumtarsa su ka yi kokawa da zaki har ya kashe shi.
Lamarin dai ya faru ne a gundumar Mpefu Kagadi na ƙasar Uganda.