Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine

0
52
Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine

Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine

Wani jirgin sojin ƙasar Rasha samfurin Mi-28 ya faɗo a wani yanki da babu kowa a Kudu maso yammacin kasar.

Hatsarin jirgin mai sauƙar ungulu ya yi ajalin ma’aikatan jirgin, kamar yadda wasu kamfanonin dillancin labaran ƙasar Rasha suka sanar a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na TASS ya ambato wata majiya a ma’aikatar tsaro ta ce “helkiwafta ƙirar Mi-28 ya fado a yankin Kaluga, ma’aikatan jirgin sun mutu.”

“Bayanan farko sun nuna wata matsalar fasaha ce ta haddasa hatsarin jirign,” in ji kamfanin dillancin labarai na Interfax, yana ambato wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutum 18

Hatsarin jirgin sojin ya faru ne  ne a wani daji mai tazarar kilomita 150 daga kan iyakar ƙasar Rasha da Ukraine, kamar yadda wani jami’in yankin ya shaida wa TASS.

Haɗarin ya afku ne a wani daji mai nisan kilomita 150 daga kan iyakar ƙasar ta Ukraine.

Leave a Reply