Wani jirgin sama a Amurka ya ɓace da mutane 10 a ciki

0
30
Wani jirgin sama a Amurka ya ɓace da mutane 10 a ciki

Wani jirgin sama a Amurka ya ɓace da mutane 10 a ciki

Ƙungiyoyin da dama ne suke gudanar da aikin binciken, ciki har da askarawan tsaron gabar teku na Amurka shiyar Alaska da rundunar kula da harkokin jiragen sama ta Alaska da kuma Sojojin tsaron kasa na Alaska da wasu kungiyoyin bincike na yankin.

Hukumomi sun ce jirgi mai saukar ungulu na musamman na Jayhawk ya taimaka da safiyar jiya Juma’a wurin binciken.

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI itama tana bada taimako wurin bada bayanan wayar salula domin gano inda jirgin yake.

Jirgin na Bering Air Caravan yana kan hanyarsa ne a yammacin Alaska, daf da kudu da Artic Circle, daga Unalakleet zuwa Nome. Rundunar jihar Alaska sun ce da misalin karfe 4 na yamma ne aka sanar da su bacewar jirgin.

Rundunar tsaron gabar tekun sun wallafa a dandalin X cewa jirgin yana nisan kilomita 19 a saman teku ne aka rasa gano inda yake.

KU KUMA KARANTA:Jirgin sama ya faɗo akan titin Sao Paulo ya kashe mutane 2

An riga an sanar da iyalan fasinjojin dake cikin jirgin, a cewa ma’aikatar kashe gobara ta Nome Volunteer amma dai ba a bayyana sunayen fasinjojin ba.

Ma’aikatar kashe gobara ta wallafa a dandalin X cewa tana gudanar da bincike mai zurfi a kasa, amma yanayi mai hazo na kawo cikas ga aikin binciken jirgin. Ma’aikatar ta bukaci jama’a da kada su kafa nasu bincike saboda yanayi mai hadari a yankin, wanda ke fuskantar dusar kankara ba zato ba tsammani da kuma iska mai karfin gaske.

Jiragen sama ne hanyoyin sufuri dake jigilar mutane tsakanin yankunan karkara na Alaska.

Jirgin da ya bace shi ne babban hatsarin jirgin sama na uku da ya faru a Amurka a cikin ‘yan kwanakin nan. A ranar 29 ga Janairu, wani jirgin sama na kasuwa da wani jirgin sama mai saukar ungulu na Sojoji sun yi karo kusa da filin jirgin saman Reagan na Washington. Bayan kwana biyu, wani jirgin daukar marasa lafiya ya yi hatsari a wata unguwar a Philadelphia jim kadan bayan tashinsa, inda ya kashe mutane shida da ke cikinsa da wani mutum a kan titi.

Leave a Reply