Wace daraja kuɗi ke da shi a wajenka?

0
226
Wace daraja kuɗi ke da shi a wajenka?

Wace daraja kuɗi ke da shi a wajenka?

Daga Yusuf Alhaji Lawan

Kuɗi ya zama muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan’adam, saboda tasirinsa a cikin dukkanin ɓangarori na rayuwa, domin biyan buƙatun yau da kullum.

Ana amfani da kuɗi domin abubuwa da dama, ciki har da kare mutunci da samun karɓuwa a wajen jama’a. Kuɗi na da amfani ga mutum domin biyan buƙatu na wajibi da samun ‘yanci, yin zaɓi da jin daɗi, da kuma ajiya, maganin wata rana. Kuɗi na bai wa mutum dama wajen taimakon marasa shi. Lallai kuɗi na taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar mutum. Misali, kuɗi na sa mutum natsuwa, kuma samun su na ba mutum damarmakin cimma buri da sauransu.

Ya zo a ruwaya cewa, “duk wanda Allah ya ba kuɗi, ya ba shi mabuɗan aljanna”. Haka ma, ya zo a cikin sanannen hadisin nan, in da talakawa suka je wajen Manzon Rahma (SAW) suna ƙorafin cewa, “masu kuɗi sun tafi da lada”. Waɗannan duka na nuni zuwa ga muhimmancin kuɗi a rayuwar mutum, shi mutum a mustaƙillin kansa da kuma rayuwarsa tare da jama’a da kuma a matsayinsa na mai imani da biyayya ga addini.

To kai mene ne ma’ana da amfanin kuɗi a gare ka? Tsakanin rayuwar ka da kuɗinka wanne ka fi so? Tsakanin ‘ya’yanka da dukiyarka wanne ne farko? Tsakanin addininka da abin da ka mallaka wanne ne a gaba? Waɗannan tambayoyi na bijiro da su ne musamman saboda yadda mutane a ɗaiɗaiku da kuma a al’ummance ke gudanar da al’amura da suka shafi kuɗaɗensu.

Mun tsinci kanmu a cikin wani yanayi na ruɗani da rashin tabbas da idanuwa suka rufe, wanda har ya kai ga rarrabe dama daga hagu na ba da wahala. Sannan kuma ga darussa da kullum rayuwa ke koyar da mu, domin mu farka daga barci, amma mun gagara ɗaukar izna, balle mu yi ƙoƙarin gyarawa.

Allah (SWT) Shi ne Ya halicci ɗan’adam, kuma ya fi kowa saninsa, a kan wannan ne Ya faɗa a wurare da dama a cikin littafinsa mai tsarki, ya yi jan hankali da gargaɗi, da kuma nusar da bayi a kan abubuwa da dama. Har ila yau, a wurare da dama Ya gabatar da kuɗi a lamurra kafin rayuka da ma ‘ya’ya da sauransu. Muna iya ɗaukar misalai kamar haka:

1. “Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya! Kada *dukiyoyinku* da *’ya’yanku* su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Dukkan waɗanda suka aikata haka, waɗannan su ne masu taɓewa.” (Al-munafiqoon 11).

2. “Hakika, za’a jarrabe ku cikin *dukiyoyinku* da ku *kanku*, kuma za ku ji munanan kalamai daga waɗanda aka ba littattafai gabaninku, kuma da waɗanda suka yi shirka. Idan kuka jure, kuma kuka ji tsoron Allah, yin haka yana daga cikin manyan al’amura.”( Aali Imran 187).

3. “Ku ba da gaskiya ga Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihadi kan tafarkin Allah da *dukiyoyinku* da *kawunanku.* Wannan shi ne mafi zama alheri gare ku idan kun sani.” (As-Saf 11).

4. “Ku yi harama (jihadi), kuna marasa nauyi, ko kuma kuna masu nauyi, kuma ku yi jihadi da *dukiyoyinku* da *kawunanku*, bisa tafarkin Allah. Haka shi ya fiye muku idan kun sani.” (At-Taubah 41).

Tare da dukkan waɗannan zaburarwa, me ya sa dukiyoyinmu suke da tsada a wasu lokuta har fiye da rayukanmu ko iyayenmu ko ‘ya’yanmu ko makusantanmu? Me ya sa dukiyoyinmu suka fi addininmu daraja?

Allah Madaukakin Sarki na da fata da tsammani daga bayi, su yi amfani da dukiyar da Ya ba su domin neman Yardar sa kafin ma ba da rai.

Amma a yanzu mutum na iya sadaukar da kansa wajen kare iyalansa ko iyayensa ko ‘yan uwansa ko addininsa amma ba lallai ya iya yin makamancin hakan wajen ba da dukiyarsa ba.

KU KUMA KARANTA: Wani matashi a Kano ya kai wa yan sanda kuɗin da ya tsinta

Yin abu don Allah shi ne abin da aka fi buƙata fiye da komai domin samun sakamako a wajen Ubangiji. Wannan kuma ya fara ne tun daga sauƙe haƙƙin dukiya a kan mai ita, zuwa ga ma’abota kusancinsa da sauransu.

Ya zo a Hadisil Qudsi, Allah Yana cewa: “Dukiya, dukiya ta ce, mawadaci wakilina ne, faƙiri iyalina ne (ɗawainiyata ce), duk wanda ya hana iyalina dukiyata, zan saka shi a wuta ban damu ba”.

Wannan faɗakarwa ce ga ma’abota dukiya domin su sani cewa, shi wanda ya ba da ita, ya yi haka ne da hadafi, kuma hadafin shi ne gabatar da ita a lokutan da suka dace. Wannan kuma bai hana tattali ba, bai kuma buɗe kofar almubazzaranci ba. Domin akwai tsoratarwa mai yawa ga waɗanda Allah Ya ba su dukiya kuma suka bari ta lalace ba tare da kula da ita ba.

To, a wannan lokaci, rayuwa ta tsananta ga al’umma musamman game da wannan hali da hukuma ta zaɓi ta saka mutane a ciki na matsin rayuwa, ya kamata ya zama wata dama ga masu hanu da-shuni da su yi amfani da ita wajen taimakon marasa shi, saboda su samu sauƙi.

Su ba su gudummuwa, musamman na kuɗi ko abin masarufi ko wani abu da ya shafi kasuwanci, yin haka abu ne mai girma a wurin Allah wanda yake cike da riba. Lallai bayarwa ba ya ƙarar da dukiya, asali ma, shi ne ya ke kawo wa dukiya albarka.

Muna addu’a, Allah Ya canza mana munanan halayenmu da kyawawan halaye, Ya ba mu dacewa zuwa ga abin da ya fi soyuwa gare Shi, wanda Yake yarda da shi. Ya kuma kiyaye mu daga sharrin Shaiɗan jefaffe domin darajar ma’abota daraja a wajenSa.

Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga Unguwar Hausawa Asibiti, a garin Potiskum, jihar Yobe. Kuma za a iya tuntuɓarsa ta nasidi30@gmail.com.

Leave a Reply