Turkiyya ta la’anci farfagandar Isra’ila a kafafan sada zumunta na yanar gizo, ta sha alwashin kare Gaza

0
70

A wani martani da Turkiyya ta mayar ga wata farfagandar ministan harkokin wajen Isra’ila a shafukan sada zumunta na yanar gizo, Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sake jaddada matsayar Turkiyya ta la’antar munanan ayyukan Isra’ila kan al’ummar Gaza.

“Shugaba Erdogan na nan a kan matsayarsa ta la’antar munanan ayyuka marasa hujja da dalili da Isra’ila ke aikata wa kan jama’ar Falasɗin,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a wata sanarwa da ta fitar a hukumance a ranar Lahadi.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Yisrael Katz ya yi kalaman ƙage da ɓata suna ta hanyar yaɗa tsokacin Shugaba Erdogan game da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

KU KUMA KARANTA: Shugaban Turkiyya ya gana da jami’an tsaron Poland da Romania a Ankara

Sanarwar ta ce Turkiyya ta ƙudiri niyyar kawo karshen ‘kisan kiyashin’ da Tel Aviv ke yi, kuma na neman ganin ‘an mayar da Isra’ila saniyar ware’ a matakin ƙasa da ƙasa.

“Wannan ne ya sanya wasu ‘yan siyasar Isra’ila suke harar Shugaban Ƙasar Turkiyya Erdogan ta siga marar ladabi,’ in ji sanarwar.”

Ma’aikatar ta ce matakan Isra’ila na sanya ‘barazana’ ba su tsaya ga Falasdinawa kawai ba, har ma sun kai ga ‘yan Isra’ilan kansu.

“Sanarwar ta kuma bayyana muhimmancin yin ƙarin haske kan “manufofin nuna wariya da rashin adalci” da Isra’ila ke ɗabbaka wa kan Falasdinawa.

Ta ƙara da cewa “Turkiyya za ta kare muradun falasdinawa har zuwa lokacin da za su mallaki ƙasarsu, a cikin ƙasarsu.”

Ankara na sukar matakan amfani da karfi da Tel Aviv ke yi, inda wasu ‘yan siyasar Isra’ila ke yin suka marar tushe balle makama ga Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Leave a Reply