Connect with us

Ƙasashen Waje

Turkiyya na fatan bunƙasa kasuwanci da Saudiyya zuwa dala biliyan 30

Published

on

Ƙasar Turkiyya na fatan bunƙasa harkokin kasuwancinta da ƙasar Saudiyya zuwa $30b a matsakaicin zango, kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz ya faɗa a wajen wata walimar cin abincin dare da aka shirya ta taron zuba jari tsakanin Tukiyya da Saudiyya da aka yi a birnin Istanbul.

A wajen walimar da aka gudanar ranar Alhamis, Yilamz ya ce cinikayyar da aka yi tsakanin ƙasasahen biyu ta kai ta $6.8B a 2023, yayin da kamfanonin Saudiyya suka zuba jari da ya kai na dala biliyan biyu a Turkiyya kawo yanzu.

“Muna ganin za mu iya burin bunƙasa yawan cinikayyar da muke yi ta yadda kowane ɓangare zai amfana kuma cikin sauri zuwa dala biliyan 10 cikin gajeren zango, a cewarsa.

KU KUMA KARANTA: Burin Turkiyya shi ne samun cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi – Shugaba Erdogan

Yilmaz ya ce Turkiyya na sawun gaba a matsayin nahiya, wajen fitar da kaya da zuwa jari tun bayan annobar korona.

“Turkiyya na ba da dama ga masu zuba jari a fannin kimiyya, da tsaro, da samar da makamashi da ba ya gurɓata mahalli, da harkokoin albarkatun man fetur, da harkar kuɗaɗe, da yawon buɗe ido, da kuma gine-gine a matsayin wani ɓangare na zuba jari na ƙasa da ƙasa,” kamar yadda ya fada.

“Ɓangarorin Saudiyya da suka yi wa masu jari bayani sun haɗa da sinadarai, masu ƙere-ƙeren injina, da masana’antun sarrafa abinci da kayan shaye-shaye, da sababbin fasahohi, da harkokin abubuwan hawa, da ɓangaren jiragen sama da magunguna, da kayan kula da lafiya, da harkokin soja, da makamashin da ba ya gurɓata mahalli, da kayan gine-gine, da kuma harkar haƙar ma’anadanai,” a cewarsa.

Dangane da ganawarsa ministan yawon buɗe ido na Saudiyya Ahmed AlKhateeb kuwa, Yilmaz ya ce “mun nuna gamsuwa da yadda adadin masu zuwa Turkiyya yawon buɗe ido daga Saudiyya ya ƙaru zuwa kaso 70 a 2023, inda ya kai kimanin 830,000, mun kuma yi duba kan adadin ƴan ƙasarmu dake ziyarar Saudiyya daga Turkiyya da ya ƙaru fiye da sau uku da rabi, inda ya kai mutum 670,000 a 2023.

“Mun kuma amince gaɓa ɗaya cewa ya kamata a sake duba damammakin da ake da su a fannin yawon bude ido tsakanin Saudiyya da Turkiyya,” kamar yadda ya bayyana.

Yilmaz ya ƙara da cewa, gudunmuwar da alaƙar ƙut-da-ƙut kuma tattaunawa mai ƙarfi ta siyasa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu za su bayar a fannin haɗakarmu ta tattalin arziki, za su ƙara inganta haɗakarmu.”

“Yayin da Turkiyya za ta ci gaba da bai wa masu zuba jari ƴan Saudiyya muhimman damammaki, Saudiyya ita ma ta ci gaba da samar da muhimman yanayi mai kyau ga masu zuba jarinmu na Turkiyya,” a cewarsa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Published

on

Dakta Mas'ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Daga Ibraheem El-Tafseer

Waye Dakta Mas’ud Pezeshkian sabon shugaban ƙasar Iran na 9 cikin shekaru 45 ataƙaice?

An haife shi a ranar 29 ga Satumba, 1954, a Mahabad, a yammacin lardin Azarbaijan, Dakta Mas’ud Pezeshkian ya wakilci birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar a majalisar dokokin Iran ta 12.

Ya riƙe muhimmin muƙamai a majalisar a Hukumomi daban-daban matakin gwamnatin tarayya, kuma ya zama ministan lafiya a lokacin mulkin Shugaba Mohammad Khatami (2001-2005). Duk da cewa an tsige shi bayan wasu lokuta saboda gaza cimma wasu ayyuka da kawo sauyi.

An zaɓe Pezeshkian a majalissar 8th, 9th, 10th, and 11th. A tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban majalisar na farko. A baya dai ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2013 da 2021 amma ya kasa samun nasara a lokuta biyun.

KU KUMA KARANTA: An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Dr. Mas’ud Pezeshkian likitan zuciya ne kuma me koyarwa, ya yi aiki a matsayin shugabar Jami’ar Tabriz ta Kimiyyar kiwon lafiya, kuma a halin yanzu memba ne na ma’aikatan ilimi a wannan babbar jami’a a arewacin Iran.

Bayan da ya samu amincewa daga babbar hukumar da ke sa ido kan zabukan kasar na ya tsaya takara a zaben na ranar 28 ga watan Yuni a watan da ya gabata. Ya gabatar da tsare-tsarensa, inda ya jaddada muhimmancin damka ayyuka ga kwararru kuma masu ilimi a gwamnatinsa.

Haka nan kuma ya bayyana Javad Zarif, tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran a matsayin zabinsa na shugabancin ma’aikatar harkokin wajen kasar, yayin da ya sha alwashin aiwatar da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Pezeshkian a hukumance ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasar a ranar 1 ga watan Yuni, rana ta uku ta rajista, a ma’aikatar harkokin cikin gida da ke Tehran, tare da rakiyar gungun magoya bayanta.

A muhawarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, Pezeshkian ya bayyana mahimmancin kiyayewa da cika alkawura a matsayin wani muhimmin al’amari na kiyaye kyawawan halaye.

Ya jaddada muhimmancin nuna girmamawa ga daidaikun mutane, tabbatar da jin muryoyinsu, da bayar da shawarwari kan ayyuka bisa ka’idojin adalci da adalci.

Tsohon ministan lafiya ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da amana ke takawa wajen ciyar da al’umma gaba, tare da jaddada cewa gaskiya na da matukar muhimmanci wajen samar da amana a tsakanin al’umma.

Pezeshkian ya jaddada muhimmancin ba da fifiko kan dangantaka da kasashen dake makwabtaka da ita, da fadada huldar dake tsakanin kasashen duniya don bunkasa ci gaban kasar.

A lokuta da dama, ya nanata kudurinsa na mutunta tsarin dokokin Jamhuriyar Musulunci da kuma manufofin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene ya bayyana.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Published

on

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra'ila

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar Hezbollah mai da ke Lebanon ta ƙaddamar da hare-haren rokoki fiye da 200 da jirage marasa matuƙa zuwa arewacin Isra’ila, a wani martani na kisan ɗaya daga cikin manyan kwamandojinta.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojanta da dama a hare-haren, na Hezbollah.

Sojojin na Isra’ila sun kuma ce sun mayar da martani kan mayaƙan ƙungiyar da sansanoninta da ke kudancin Lebanon.

Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ce mutum guda ya mutu a wani harin jirgi maras matuƙi da Isra’ila ta kai garin Houla.

Hare-haren na baya-bayan nan, sun kasance mafiya muni cikin watanni tara tsakanin kan iyakokin ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

An kashe ɗaya daga cikin kwamandojin Hezbollaha wani hari ta sama da Isra’ila ta kai birnin Tyre na ƙasar Lebanon.

Mohammed Nimah Nasser, ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin ƙungiyar, kafin kisan nasa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

Published

on

Wani jirgin ruwa ya kife da 'yan ci-rani a tekun Mauritania

Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

‘Yan ci-rani kimanin 90 ne suka rasu a kan hanyarsu ta zuwa Turai a lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a farkon makon nan a gabar tekun Mauritania, in ji kafar watsa labarai ta ƙasar wadda ta ambato jami’ai na bayani a ranar Alhamis.

Ana kuma ci gaba da neman da dama da suka bata.

“Jami’an tsaron teku na Mauritania sun gano gawawwakin mutane 89 da suka hau wani babban jirgin ruwan masunta da ya kife a ranar Litinin 1 ga Yuli a gabar tekun Atlantika,” kusan nisan kilomita huɗu daga gabar garin Ndiago a kudu maso-yammacin kasar, in ji kamfanin dillancin labarai na Mauritania a ranar Alhamis.

Jami’an tsaron iyakokin tekun sun kuma kuɓutar da wasu mutanen tara, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara biyar, in ji kafar yaɗa labaran.

Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa wadanda suka kuɓuta na cewa jirgin nasu ya taso ne daga iyakar Senegal da Gambia dauke da fasinja 170, wanda hakan ya sanya ake neman mutane 72 da suka ɓata.

Wani babban jami’in karamar hukuma a yankin da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar wa AFP aukuwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: Jirgin sojin Najeriya ya faɗo a Kaduna

Hanyar tekun Atlantika na da hatsari sosai saboda manyan igiyar ruwa, kuma ‘yan ci-rani na yin lodin da ya haura ka’ida a jiragen ruwa, a mafi yawan lokuta jiragen ba su da ingancin shiga teku, kuma ba sa ɗaukar isassen ruwan sha.

Amma hakan ya sake fitowa fili ne sakamakon yadda ake ƙara sanya idanu kan tekun Bahar Rum.

A shekarar 2023 adadin ‘yan ci-rani da suke zuwa tsibiran Canary na Sifaniya ya ninka a shekara guda, wanda ya kai mutane 39,910, kamar yadda gwamnatin Sifaniya ta bayyana.

Tsibiran Canary na Sifaniya na daura da iyakar tekun arewacin Afirka da nisan kilomita 100.

Amma jiragen ruwa da dama – mafi yawansu na katako – na kama hanya daga Maroko, Yammacin Sahara, Mauritania, Gambia da Senegal don zuwa tsibiran na Sifaniya.

Sama da ‘yan ci-rani 5,000 ne suka mutu a teku yayin ƙoƙarin tsallaka wa Sifaniya a watanni biyar na farkon wannan shekarar, kenan mutane 33 ne ke mutuwa kowacce rana, kamar yadda Caminando Fronteras, wata ƙungiyar bayar da agaji ta Sifaniya ta bayyana.

Wannan ne adadin rasa rayuka mafi yawa tun bayan da kungiyar ta fara tattara bayanai a 2007, kuma mafi yawa na mutuwa ne a hanyar tekun Atlantika.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like