Tubabben ɗan daba a kano, ya zama jami’i mai kama masu laifi

0
260

Tubabben ɗan daba mai suna Chile Mai Doki ya kammala ɗaukar horo na zama ɗan sandan sarauniya, wato Constabulary a Kano.

Wato daga aikata laifuka ya koma mai kama masu aikata laifuka.

Idan zaku iya tunawa Chile Mai Doki na ɗaya daga cikin ‘yan daban da runudnar ‘yan sanda a Kano ta ce ta na nema, har ma ta sanya tukuicin naira dubu ɗari (100,000) ga wanda ya kawo ɗaya daga cikin su, ya tuba, ya kai kan sa ga rundunar.

Matashi Chile Mai Doki, na daga cikin waɗanda rundunar ‘yan sanda ke nema idanu rufe, bayan gano yadda suke hana zaman lafiya da tayar da tarzoma a Kano.

KU KUMA KARANTA: Wasu da ake nema ruwa a jallo, sun miƙa wuya ga ‘yan sanda a Kano

Sai dai bayan ɓullar wani bayani, wanda ke nuni da neman mutanen idanu rufe, ya sa Chille ya kai kansa, kuma ya ce ya tuba, har ma da alƙawarin zai ba da gudunmawa wajen zaman lafiya a Kano.

Chille ya bayyana cewa, ya koma rayuwa a maƙabarta musamman ɓangaren kwana, saboda gujewa kamun ‘yan Sanda, kafin daga bisani ya yanke shawarar miƙa kan shi.

Zuwa yanzu dai, Chille ya shiga kundin tubabbun ‘yan daba a jihar Kano.

Leave a Reply