Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya
An sanar da rasuwar tsohon shugaban alƙalan Najeriya, mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, yana da shekaru 71 a duniya.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar Bauchi ta fitar, wadda ta samu sa hannun Mukhtar Gidado, mai magana da yawun gwamnan jihar Bala Mohammed, ta ce “Tanko ya rasu ne yau a ƙasar Saudiyya bayan fama da doguwar jinya.”
Tanko Muhammad, ɗan asalin jihar Bauchi ya riƙe muƙamin shugaban alƙalan Najeriya ne daga shekarar 2019 zuwa 2022 ƙarƙashin tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari.
KU KUMA KARANTA: Kotu a Abuja ta kori ƙarar da aka shigar don hana ICPC bincikar badaƙalar tallafin karatu na gwamnatin Kano
Haka kuma ya taɓa zama alƙalin Babbar Kotu, da Kotun Ɗaukaka ƙara da kuma Kotun Ƙoli ta Najeriya.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana rasuwar mai shari’a Ibrahim Tanko a matsayin “babbar hasara ga Najeriya baki ɗaya”.









