Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC, ya tabbatar da komawarsa jam’iyyar SDP
Hakan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan raba gari da jam’iyyar APC.
A ranar Litinin ne tsohon gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce: “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.
KU KUMA KARANTA:El-Rufai ya kai ƙarar Majalisar Dokokin Kaduna kotu
Ya ziyarci ofishin jam’iyyar ta SDP tare da yankan katin zama ɗan jam’iyya.
Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka ƙirƙire ta.”
Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.