Tsoffin Kuɗi: Buhari ne ya bada umarni ƙarin kwana 10 – CBN

0
424

Babba bankin Najeriya ya ƙara wa’adin canza tsohon kuɗin na naira.

Godwin Emefiele, gwamnan bankin, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada izinin ƙara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

“Wa’adin dawo da tsoffin takardun kuɗi na naira 200, 500 da 1000 ya rage ranar 31 ga watan Janairu, 2023,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na twitter.

A cikin faifan bidiyon, Emefiele ya ce, “Abin takaici, ba ni da labari mai dadi ga waɗanda suke ganin ya kamata mu sauya wa’adin. Dalili kuwa shi ne, kamar yadda shugaban kasa ya faɗa fiye da sau biyu, har ma da wasu a ɓoye, kwana 100 ya fi wanda ya mallaki tsohon kuɗi ya ajiye a bankuna.

KU KUMA KARANTA:Mun bada isasshen lokaci don haka babu ja da baya kan daina karɓar tsoffin kuɗi- CBN

Kuma mun ɗauki kowane mataki don tabbatar da cewa dukkan bankunan sun kasance kuma har yanzu a buɗe suke don karɓar kuɗaɗen ajiya.”

Ya ce ya zuwa yanzu, CBN ya tara tiriliyan 1.9 sannan ya bayar da biliyan 900 domin cimma nasarar aiwatar da manufofin. Ya ce ’yan Najeriya da har yanzu ba su sauya takardar kuɗin Naira daga tsohuwar zuwa sababbi ba, yanzu sun samu damar yin hakan.

Gwamnan babban bankin ya yi gargaɗin cewa dole ne mutane su yi amfani da damar domin ba za a sake tsawaita wa’adin ba.

“Bisa abubuwan da suka gabata, mun nemi kuma mun samu amincewar shugaban ƙasa kan waɗannan abubuwa: ƙarin kwanaki 10 na wa’adin daga ranar 31 ga Janairu, 2023, zuwa 10 ga Fabrairun 2023; don ba da damar tattara ƙarin tsofaffin takardun bayanan da ‘yan Najeriya ke riƙe da su da kuma samun ƙarin nasara wajen musayar kuɗi a cikin yankunan karkara.

“Ma’aikatan CBN din mu a halin yanzu da suke gudanar da taro da sa ido tare da jami’an EFCC da ICPC za su yi aiki tare domin cimma waɗannan manufofin.

“Wa’adin kwanaki 7, daga ranar 10 ga Fabrairu zuwa 17 ga Fabrairu, 2023, wanda ya dace da sashe na 20 (3) da 22 na dokar CBN, wanda ya baiwa ‘yan Najeriya damar ajiye tsofaffin takardunsu a bankin CBN bayan wa’adin watan Fabrairu lokacin da tsohon ya yi da kudin zai rasa matsayinsa na Legal Tender,” in ji CBN a cikin wata sanarwa.

A shekarar da ta gabata ne Babban Bankin kasar ya gabatar da sabon tsarin takardar kudi na Naira 200, 500 da 1000 tare da bayar da wa’adin ranar 31 ga watan Janairu, 2023 don musanya takardun kudi.

An dai sha matsin lamba ga babban bankin kan ya sauya wa’adinsa na ƙaranci sabbin takardun kuɗi na Naira amma har zuwa daren ranar Asabar, bankin ya sha alwashin ba zai yi hakan ba.

Leave a Reply