Tsawa ta kashe mutane 14 a wani sansanin ‘yan gudun hijira

0
50
Tsawa ta kashe mutane 14 a wani sansanin 'yan gudun hijira

Tsawa ta kashe mutane 14 a wani sansanin ‘yan gudun hijira

Aƙalla mutane 14 da suka haɗa da yara da dama ne suka mutu a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Uganda bayan tsawa ta afkawa wani cocin wucin gadi da suka fake a lokacin wata mummunar gugguwa, kamar yadda jami’an yankin suka sanar a jiya.

Kimanin mutane 50 ne suka fake a majami’ar sansanin ‘yan gudun hijira na Palabek da ke arewacin Uganda a yammacin ranar Asabar lokacin da wata mummunar guguwa ta afkawa yankin.

Mutane 14 ne suka mutu a lokacin da walkiya ta afkawa rufin ƙarfen cocin na wucin gadi da suka haɗa da ‘yan mata biyar da kuma yara maza 9 masu shekaru tsakanin 14 zuwa 18, kamar yadda William Komech, jami’in gundumar Sao Paulo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

KU KUMA KARANTA: Walƙiya da tsawa ta kashe sayar da shayi a jihar Kwara

‘Yan gudun hijirar galibinsu ‘yan ƙabilar Nuer ne na Sudan ta Kudu.

“Gwamnati tana aiki tare da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) da sauran hukumomi don ba da agajin da ya dace ga wadanda suka tsira,” Hillary Onek, ministar ‘yan gudun hijira da shirye-shiryen Uganda, ta shaida wa AFP.

Uganda ta fuskanci mace-mace masu nasaba da walƙiya a cikin ‘yan shekarun nan. A shekarar 2011 ne, walkiya ta afkawa wata makarantar firamare, inda ta kashe dalibai akalla 18 da matasa tara.

Leave a Reply