Connect with us

Labarai

Tinubu ya umarce ni in riƙa faɗin gaskiya – Idris

Published

on

Tinubu ya umarce ni in riƙa faɗin gaskiya – Idris

Tinubu ya umarce ni in riƙa faɗin gaskiya – Idris

Daga Idris Umar, Zariya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarce shi ne da ya dawo da amana da gaskiya a aikin yaɗa labaran gwamnati ga jama’a.

Idris ya bayyana haka ne a Abuja a wajen bikin cika shekaru 60 da kafa Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa (NIPR)

A taron, mai taken “Hulɗa da Jama’a: Farfaɗo da Ƙima da Sauyin Tattalin Arziki”, ministan ya ce: “Shugaba na, Shugaba Bola Tinubu, wanda ya naɗa ni, ya amince in faɗi abubuwa yadda suke, amma cikin yanayi mai daɗi.

“Ya ba da umarnin cewa dole ne a dawo da amana ga aikin sadarwar jama’a.

“Hakan ne kawai mutane ko ’yan ƙasa za su mutunta kuma a ko yaushe su so sauraron gwamnati.

“Za mu ci gaba da yin hakan har zuwa ƙarshen aiki na a nan.”

A cewar ministan, yana da kyau a ko da yaushe a gaya wa jama’a gaskiya, su ma su gane cewa kana gaya masu gaskiya ne.

Ya ce: “Dole ne a dawo da amana da gaskiya a cikin aikin sadarwar jama’a.

“Don haka, idan ba ni da bayani game da wani abu, zan gwammace in rufe baki na, maimakon in faɗi abin ba daidai ba.”

Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Laberiya, Dakta Jewel Taylor, a cikin jawabin ta a taron, ta ba da labarin abin da ta fuskanta na ƙyama, suka, da canza labari da mugun tunanin mutane game da ita lokacin suna kan mulki.

Taylor ta yaba wa NIPR, inda ta ƙara da cewa rayuwar ‘yan siyasa ta ta’allaƙa ne kan magance rikice-rikice, don haka hulɗa da jama’a ya kasance makami mai inganci don tunkarar matsalolin.

Ta ƙara da cewa hulɗa da jama’a abu ne da ake yi a Afrika tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka inda ake amfani da ganguna daban-daban wajen sadar da saƙo ga jama’a.

Da yake karɓar baƙi a wajen taron, Shugaban hukumar ta NIPR, Dakta Ike Neliaku, ya ce domin murnar zagayowar ranar, cibiyar ta dasa bishiyoyi 60 a kowace jiha a jihohi 36 na tarayyar ƙasar nan domin magance sauyin yanayi.

KU KUMA KARANTA: Shekara ɗaya tayi wa Tinubu kaɗan ya warware matsalolin da ya gada – Sarki Sanusi

A cewar Neliaku, aikin hulɗa da jama’a na da matuƙar muhimmanci ga sake farfaɗo da ƙima da kuma sauyin tattalin arziki.

Ya jaddada ƙudirin cibiyar na samar da labari mai kyau ga Najeriya.

Shi ma da yake jawabi, shugaban NIPR na farko, Mazi Okereke, ya ce abin da ya jawo wasu rikice-rikice a ƙasar nan shi ne taɓarɓarewar sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.

Ya ce: “Ya kamata gwamnatin Najeriya ta sanya aikin hulɗa da jama’a a kan kujerar tuƙi. Mun ji daɗin cewa ɗaya daga cikin mu yanzu ya zama Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.”

A cikin saƙon sa na fatan alheri, Shugaban Gidan Talbijin na Ben TV da ke London, Mista Alistair Soyode, ya yi kira ga NIPR da ta kafa rassan ta a wasu ƙasashen duniya domin kula da ‘yan Nijeriya da ‘yan Afrika mazauna ƙasashen waje.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya jawo hankulan masu ruwa da tsaki daga gida da waje yayin da wasu fitattun mutane suka tattauna kan batun “yin amfani da hulɗa da jama’a don bunƙasar tattalin arziki”.

Haka kuma ya ruwaito cewa ɗaliban makarantar African International School da ke unguwar Asokoro a Abuja sun rerayo waƙar haɗin kai ta fitaccen mawaƙi Temi Dakolo a wurin taron.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like