Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Kano zuwa sunan Yusuf Maitama Sule
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
KU KUMA KARANTA:An rufe jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai
Idan za a iya tunawa dai Sanata Mai Wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau Jibrin ne ya nemi a sauya sunan jami’ar a ƙarshen shekarar 2024, jim kaɗan bayan da Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mayar wa da Jami’ar jihar sunanta na asali wato ‘Northwest’.
Onanuga ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya ga dacewar maida sunan makarantar zuwa na Danmasani duba da irin ƙwazon sa na ci gaban Nijeriya kuma hakan zai zama abin tunawa ga al’umma.