Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin kuɗin 2025
Shugabn Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin kasafin 2025 na naira tiriliyan 54.99 zuwa doka.
Tinubu ya rattaba hannun ne a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja a jiya Juma’a.
KU KUMA KARANTA:Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin 2025 kan naira tiriliyan 54
An kara adadin kudin dake cikin kudirin da Shugaba Tinubu ya gabatar kuma rattaba hannu ya gudana ne a wani kwarya-kwaryan biki daya gudana a ofishinsa.