Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya naɗa Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Sabbin Hafsoshin tsaro sun gana da Ministan tsaro, Badaru
Shugaban ƙasar ya sanar da wannan naɗin ne cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata, bayan murabus ɗin tsohon ministan, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, a ranar Litinin.









