Tinubu ya janye naɗin da ya yi wa ɗan shekara 24, a matsayin shugaban FERMA

Bola Tinubu ya soke naɗin da ya yi wa Injiniya mai shekaru 24 a duniya  Imam Kashim Imam a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA).

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba.

An sanar da naɗin Imam ne a ranar Juma’a, 13 ga Oktoba.  Shugaban ya naɗa ɗan shekaru 24 “don sabunta wa’adin shekaru huɗu (4), daidai da Sashe na 2 (3) na Dokar Gyaran FERMA, 2007”.

Naɗin ya haifar da damuwa, mutane da yawa sun ce bai da ƙwarewar da ake buƙata don aikin.

Bayan martanin, Ngelale ya ce an janye naɗin ba tare da ɓata lokaci ba.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya naɗa jigon ɗan PDP a matsayin shugaban FERMA

Duk da cewa babu wani dalili da fadar shugaban ƙasa ta bayar na ɗaukar wannan mataki, Ngelale ya ce duk sauran naɗe-naɗen da aka yi a hukumar da hukumar gudanarwa ta FERMA ba ta shafi wannan umarnin ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *