Gwamnatin Tarayya ta ce za a jinkirta buɗe sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shuɗe ta amince da kafa su.
Ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Laraba a Abuja.
Ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da buƙatar samar da ingantattun shirye-shirye na ilimi ga waɗannan jami’o’in.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’in 37 daf da ƙarshen mulkinsa.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya nemi haɗin kan jami’o’in Burtaniya uku, don bunƙasa harkar ilimi a jihar Yobe
“Da yawa daga cikin sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shuɗe ta amince da kafa su ne a ƙarshen mulki.
Bayan an yi nazari da yawa, Shugaba Tinubu ya ga ya kamata a dakatar da buɗe su tukunna.
“Hakan ba wai na nufin za a soke jami’o’in ba ne, sai dai a duba su ta fuskar ƙarfinsu da fa’idar da ɗaliban za su samu.