Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa kan hatsarin jirgin kwale-kwalen da ya faru a jihar Kwara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa hatsarin kwale-kwalen ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 da suka halarci ɗaurin aure a ƙauyen Egbu da ke ƙaramar hukumar Patigi a jihar.
“Na yi matuƙar baƙin ciki da labarin hatsarin jirgin ruwa da ya salwantar da rayukan mutanenmu a jihar Kwara.
Cewa waɗanda abin ya shafa baƙi ne a wurin wani ɗaurin aure ya sa hatsarin ya ƙara zafi.
KU KUMA KARANTA: Jirgin ruwa ɗauke da mutane sama da 100 ya kife a jihar Kwara
“Tausayina da ta’aziyyata ga iyalai da abokanan waɗanda abin ya shafa. Ina kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kwara bisa aukuwar hatsarin.
Da fatan dukkan masoyan su samu ta’aziyya, “Shugaban ya yi addu’a a cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na fadar gwamnatin jihar ya fitar.
Yayin da ya buƙaci gwamnatin jihar Kwara da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa da su duba halin da ake ciki a haɗarin jirgin ruwa, shugaba Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta duba ƙalubalen da ke tattare da safarar ruwa a cikin ƙasar nan domin tabbatar da cewa lamarin tsaro da aiki ya tabbata riƙo da.
[…] KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin a yi bincike kan hatsarin jirgin ruwa a Kwara […]