Daga Ibraheem El-Tafseer
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohin ƙasar 36, a wani mataki na rage wa ‘yan ƙasar raɗaɗin cire tallafın man fetur.
Shugaban ya amince da matakin ne a lokacin taron wata wata na kwamitin kula da asusun raba kuɗin, shiga na gwamnatin ƙasar (FAAC) da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake ya fitar, ya ce sabon asusun zai taimaka wa jihohin ƙasar wajen zuba jari a ɓangarorin sufuri da harkokin noma da gina tituna da kasuwanni da kiwon dabbobi da ɓangaren lafiya da ilimi musamman a matakin farko, da wutar lantarki da ruwan sha domin haɓaka tattalin arzƙi da samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasar.
KU KUMA KARANTA: Tinubu na neman majalisa ta amince da kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
Kwamitin ya kuma amince da ajiye wani ɓangare na kuɗin da ake rabawa a kowane wata domin taƙaita tasirin ƙaruwar shiga da za a iya samu sakamakon matakan cire tallafin mai da daidata farashin dala tare da hauhawar farashin kayayyaki za su iya haifarwa.
Kwamitin ya ce daga cikin naira tiliyan 1.9 na kuɗin shigar da aka samu a watan Yunin 2023, naira biliyan 907 ne kawai za a raba tsakanin matakan gwamnatin ƙasar uku, yayin da za a ajiye naira biyan 790 a asusun.
Waɗannan kuɗaɗen da za a riƙa ajiyewa za su taimaka wajen samar da asusun gina ababen more rayuwa tare da aiwatar da wasu abubuwa, domin tabbatar da an yi amfani da kuɗin tallafin wajen gina muhimman abubuwan ci gaba, domin inganta rayuwar ‘yan ƙasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma kwamitin ya yaba wa shugaban ƙasar bisa matakin cire tallafin man tare da ɓullo da matakai daban-daban na tallafa wa ‘yan ƙasar domin rage masu raɗaɗin cire tallafin.