Tinubu ya amince da ajiye aikin Ngelale

0
206
Tinubu ya amince da ajiye aikin Ngelale

Tinubu ya amince da ajiye aikin Ngelale

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ajiye aiki da Cif Ajuri Ngelale ya yi a matsayin mai magana da yawunsa.

A safiyar ranar Asabar, Ajuri ya ba da sanarwar cewa zai tafi hutu na dindindin don tunkarar yanayin rashin lafiya da ya ce “a halin yanzu yana shafar iyalinsa”.

Ya ce ya miƙa takarda ga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Asabar, fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu ya karɓi takardar kuma ya gode wa Ngelale kan hidimar da ya yi wa ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki

“Shugaban ya karɓi takardar daga Cif Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a da kuma mai magana da yawun shugaban ƙasa da kuma wakilin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin sauyin yanayi, inda ya sanar da matakin da ya ɗauka na tafiya hutu bisa wasu dalilai na rashin lafiya.

“Shugaban ƙasa ya amince da dalilansa na hutun, ya fahimce su sosai kuma yana tausayawa al’amuran da suka kai ga yanke wannan hukunci mai wuya.

“Yayin da yake mika addu’o’insa da fatan alheri ga Cif Ngelale da iyalansa a wannan lokaci mai cike da kalubale, Shugaban na fatan samun sauki cikin gaggawa da kuma cikakkiyar lafiya,” in ji sanarwar.

Leave a Reply