Tinubu ya aike da ta’aziyar mutuwar uban ƙasa, dattijo Musa Musawa

2
344

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar ɗaya daga cikin dattawan ƙasa Alhaji Musa Musawa.

An haife Marigayin a ranar 1 ga Afrilun shekarar 1937,ya kasance mai watsa labarai, jami’in diflomasiyya, kuma hazikin ɗan siyasa. Ya rasu ne a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Alhaji Musa Musawa ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama da sauran ‘yan uwa da suka haɗa da mataimakiyar mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Barista Hannatu Musawa.

KU KUMA KARANTA: Kano Pillars na jimamin mutuwar tsohon ɗan wasanta ƙofarmata

A cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar talata ta bakin ɗaya mai taimaka masa ta fuskar yaɗa labarai, Abdul’aziz Abdul’aziz, Asiwaju Tinubu ya bayyana marigayin ɗan jihar Katsina a matsayin ɗaya daga cikin mataimakan ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kai na Najeriya.

“Haƙiƙa shi mutum ne mai son ci gaba da faɗin albarkacin bakinsa, tun yana matashi ya haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da takwarorinsa masu ra’ayi ɗaya a rusasshiyar ƙungiyar NEPU wajen fafutukar ƙwato ‘yancin kai da ƙwato ‘yancin jama’armu baki ɗaya.

“A shekarun baya bayan samun ‘yancin kai, Alhaji Musa Musawa ya ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyi masu ci gaba a ciki da wajen siyasa domin ciyar da talakawa da waɗanda ake zalunta gaba a cikin al’umma.

“Ya kasance ɗan siyasa mai ci gaba wanda ya biya hakkinsa a matsayinsa na mai kishin ƙasa.

“Najeriya ta yi rashin haziƙin da kuma za mu yi kewar shawararsa ta uba a lokacin da muke buƙata,” in ji Tinubu.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya roki Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa dattijon da ya rasu, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jumre rashin.

2 COMMENTS

Leave a Reply