Connect with us

Ta'aziyya

Tinubu ya aike da ta’aziyar mutuwar uban ƙasa, dattijo Musa Musawa

Published

on

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar ɗaya daga cikin dattawan ƙasa Alhaji Musa Musawa.

An haife Marigayin a ranar 1 ga Afrilun shekarar 1937,ya kasance mai watsa labarai, jami’in diflomasiyya, kuma hazikin ɗan siyasa. Ya rasu ne a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Alhaji Musa Musawa ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama da sauran ‘yan uwa da suka haɗa da mataimakiyar mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Barista Hannatu Musawa.

KU KUMA KARANTA: Kano Pillars na jimamin mutuwar tsohon ɗan wasanta ƙofarmata

A cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar talata ta bakin ɗaya mai taimaka masa ta fuskar yaɗa labarai, Abdul’aziz Abdul’aziz, Asiwaju Tinubu ya bayyana marigayin ɗan jihar Katsina a matsayin ɗaya daga cikin mataimakan ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kai na Najeriya.

“Haƙiƙa shi mutum ne mai son ci gaba da faɗin albarkacin bakinsa, tun yana matashi ya haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da takwarorinsa masu ra’ayi ɗaya a rusasshiyar ƙungiyar NEPU wajen fafutukar ƙwato ‘yancin kai da ƙwato ‘yancin jama’armu baki ɗaya.

“A shekarun baya bayan samun ‘yancin kai, Alhaji Musa Musawa ya ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyi masu ci gaba a ciki da wajen siyasa domin ciyar da talakawa da waɗanda ake zalunta gaba a cikin al’umma.

“Ya kasance ɗan siyasa mai ci gaba wanda ya biya hakkinsa a matsayinsa na mai kishin ƙasa.

“Najeriya ta yi rashin haziƙin da kuma za mu yi kewar shawararsa ta uba a lokacin da muke buƙata,” in ji Tinubu.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya roki Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa dattijon da ya rasu, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jumre rashin.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: An harbe babban malamin Shi’a na Majalisar Ƙwararrun Iran | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Yadda mutuwar Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta jijjiga Kannywood | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ta'aziyya

Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a ranar arba’in

Published

on

Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a ranar arba’in

Daga Ibrahim Sheme

  1. Al-Mujibu ka ba ni tanyo,Zantuka domin in shiryo,Ba gwaninta ai a koyo,Addu’a ce za ni ɗan yo,Ta rashin ‘yar’uwar mu Daso.
  2. Gaisuwa ta ta taƙaita,Gun mafificin halitta,Ɗaha mai zurfin fahimta,Ɗan Amina uba ga Binta,Wanda tai ƙaunar sa Daso.
  3. Mutuwa mai wafce kaɗo,‘Yar Fulani ce ta fyaɗo,Saratun mu ɗiyar Giɗaɗo,Ba sanarwa ta saɗaɗo,Ta yi wuf da ƙawar mu Daso.
  4. Saratun mu ɗiyar Muhamman,‘Yar Kano ce ita wannan,Jaruma a Kannywood sannan,Ayyukan ta a duniyar nan,Sun yi tasiri da naso.
  5. Tun da farko rayuwar ta,Ta yi ticin makaranta,‘Yan firamare fa mata,Har mazan duk ta ƙagauta,Gun batun koyon su, Daso.
  6. Sai ta tsoma ƙafa a harkar Shirya fim ku ji don ku sadar,Kamfanin su Sarauniya har,Masu barci duk ta farkar,Masu so har wanda bai so.
  7. Tai fice a finafinan mu,Mun gani a akwatunan mu,Can ta hasko rayuwar mu,Dariya ta saka a ran mu,In tana aktin ta Daso.
  8. Masu fim kaf ba kamar ta,In mugunta suka sa ta,Kishiya ko ko uwar ta,Za ta yi shi iya gwaninta,Yadda daraktan ta ke so.
  9. Shi fa rol in dai ta taka,In na kirki babu shakka,Ko na assha ne ta tafka,Sai a ce, “Allah ya saka,Ya biya burin ki Daso.”
  10. Ban da fim ɗin, kar ku manta,Gun ciyarwa kun fa san ta,Tallafin duk mai buƙata,Yara, tsofaffi da mata,Ko a nan lada ta kwaso.
  11. Tai rabo na ruwa, abinci,Masu so a gare ta sun ci,Ga tufafi – har ga zuci –Ta kira mai shara barci:“In kana so, to ka taso.”
  12. Ran da Ramadan ya ƙare,Malamai suka ce a daure,Ai talatin kar a sare,Shi ta ɗauka don ta more,Don cikar ladar ta Daso.
  13. Tai shirin Sallah da maiƙo,To ashe da akwai fa saƙo,Ba daɗewa ta yi baƙo,Ran ta ne aka ce ya miƙo,Ya taho, haka Hayyu ke so.
  14. Tai sahur, sallah, ta kwanta,Sai ta ce, “Bari dai na huta,”Rabbana ya katse zaman ta,Can da hantsi ‘yar’uwar ta,Tai kira, ai ba ta taso.
  15. Duk gari kowa ya ruɗe,Zuciyoyi suka bauɗe,Lamarin jama’a ya cuɗe,Duk kalar kowa ta koɗe,Ko zuma ma ba ta laso.
  16. Duk masoya sun saduda,Dandazon jama’a mashaida,Sun yi sallar ta a Fada,Daga nan tafiya ta idaGun kushewa tata Daso.
  17. An rufe ta ana ta kuka,Turbuɗe ta akai a laka,Zuciyoyi na ta duka,Sai du’a’i ke ta sauka:“Al-Gaffar yafe wa Daso!”
  18. Na yi kuka har a ƙalbi,Na siƙe a wajen jawabi,Nai diƙin a wannan babi,Ba ni don in wanke gurbi:Sabulu da ruwa da soso.
  19. Addu’ar mu tutur gare ta:Zuljalalu ka jiƙan ta,Baɗinin ta da zahirin ta,Yafe dukkan kurakuran ta,Sa ta Aljannar ka, Daso.
  20. Muna ta roƙo gun Ta’ala:Yafe laifukkan ta Jallah,Kuskuren da ita ta ƙulla,Don cikar azumi da sallah,Ba ta duk rahamar ka, Daso.
  21. Arba’in yau tun rashin ta,Mun yi jimami a kan ta,Gaisuwar mu ga ‘yan’uwan ta,Har da ‘yan Kannywood zumun ta,Don rashin sistar su, Daso.
  22. Malamai ai sun ishara:Yadda Maiduka duk ya tsara,Ba tsimi kuma ba dabara,Ƙaddara ce babu gyara,Sai abin da Ƙahharu ke so.
  23. Mu da ke nan ba mu kuri,Duk daɗewa ko ko sauri,Ko da rama ko da kauri,Ko da zaƙi ko da bauri,Za mu je mu ishe ta Daso.
  24. Wagga waƙar ba bajinta,Iro ɗan Mamman ya yi ta,Sheme mai Binta da Binta,Har ku sa Auta ta Mata,Addu’a ce don ta Daso.
  25. Baituka ashirin na jera,Sai biyar a sama na ƙara,Don cikar roƙon Tabara,Na yi roƙon ba gadara,Don biɗar rahama ga Daso.
    Alhamdu lillahi!
Continue Reading

Ta'aziyya

Tawagar gidan Rediyon YBC, sun je ta’aziyya a mawallafin jaridar Neptune Prime kan rasuwar mahaifiyarsa

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tawagar gidan Rediyon jihar Yobe (YBC) ƙarƙashin jagorancin babban Manajanta, Alhaji Isah Galadima, ta kai ziyarar ta’aziyya ga Dakta Hassan Gimba, Mawallafi kuma shugaban gidan jaridar Neptune Prime Network.

Da suke jajantawa, sun miƙa ta’aziyyarsu bisa rasuwar Hajiya Hafsat Ahmed Gimba, tare da bayyana rasuwarta a matsayin wani babban giɓi, ba ga ’ya’yanta kawai ba, rashi ne ga dukkan al’umma.

Da yake ƙarin haske game da irin tasirin da Hajiya ta yi ga al’umma, yana mai jaddada cewa rasuwarta rashi ce ba ga ‘ya’yanta tara da danginta kaɗai ba, har ma ga al’umma da kuma bil’adama baki ɗaya.

Hakazalika, masu watsa shirye-shiryen sun yarda da mahimmancin rayuwar da aka kashe da kuma dawwamammen gadon da ta bari.

KU KUMA KARANTA: Mahaifiyar Mawallafin Neptune Prime, Hassan Gimba, ta rasu tana da shekara 85

Daga ƙarshe suka yi addu’a ga Dakta Hassan Gimba da iyalansa, tare da addu’ar Allah ya jiƙan mahaifiyarsu da ta rasu.

Tawagar YBC ɗin, sun haɗa da Dakta Ahmed Bedu, tsohon shugaban NUJ na jihar Yobe, Malami a jami’ar Maiduguri. Sai daraktan kula da ma’aikata da gudanarwa; Alhaji Yerima Ahmed Saleh; Umar Mohammed Gaidem, Daraktan shirye-shirye; Mallam Habu Isa Sabon Layi, Mataimakin Daraktan Labarai; Baba Garba Alhaji, Babban mai kula da ɗakin ajiya; da Hassan Sama’ila.

Idan za a iya tunawa, an binne gawar Hajiya Hafsat Ahmed Gimba a ranar 8 ga watan Janairun 2024, a maƙabartar NEPA da ke ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe.

Continue Reading

Ta'aziyya

Gwamna Buni ya yiwa Gwamna Zulum ta’aziyya kan rasuwar mai magana da yawunsa

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Alhaji Mai Mala Buni CON, ya yiwa takwaransa na jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ta’aziyya bisa ga rasuwar mai magana da yawunsa Malam Isa Gusau.

A wata takardar manema labarai, da babban daraktan yaɗa labarai na Gwamna Buni ya fitar, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce, Gwamna Buni ya bayyana Gusau a matsayin jami’i mai ƙwazo wanda ya yi wa mai gidansa hidima da jajircewa da kuma dagewa a wajen aiki.

“Gusau ya ƙware wajen sarrafa bayanai a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a yankin Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno.

“Za a tuna da shi bisa jajircewarsa, da ƙoƙarinsa wajen gudanar da ayyuka, da kuma tsawon shekaru da ya yi yana yi wa gwamna da gwamnatin jihar Borno hidima,” in ji Gwamna Buni.

KU KUMA KARANTA: Mai magana da yawun gwamna Zulum, Isa Gusau, ya rasu

“Ina miƙa ta’aziyya ga mai girma ɗan’uwa na Gwamna Zulum, gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa wannan rashi da aka yi a daidai lokacin da ake buƙatar ayyukansa don tallafa wa gwamnati.” Inji Gwamna Buni.

Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma baiwa iyalansa haƙurin jure wannan rashi.

Gusau ya taɓa zama mai baiwa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima shawara kan harkokin yaɗa labarai a lokacin yana gwamnan jihar Borno kuma Gwamna Zulum ya ci gaba da tafiya da shi, wanda ya shafe kimanin shekaru biyar yana mulki.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like