Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya buƙaci majalisar dokokin ƙasar da ta ƙyale shi ya nemo ƙarin fiye da dala miliyan ɗari biyar don samar da tallafi a wani mataki na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar wakilan ƙasar, shugaban ya buƙaci ‘yan majalisar da su yi wa kasafin kuɗin 2022 kwaskwarima don ba shi damar samo kuɗin.
Shugaban majalisar Tajudden Abbas, ya karanta wasiƙar a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Abin da wasiƙar ta ƙunsa shi ne akwai kuɗin a ƙasa, to amma shugaba Tinubun na fatan majalisar za ta gaggauta amincewa da wannan buƙata ta sa.
Shugaban majalisar ya sanar da cewa za a duba wannan buƙata a ranar Alhamis.
KU KUMA KARANTA: Na zaɓi na cire tallafin man fetur a ranar farko duk da babu shi a jawabina – Tinubu
A shekarar da ta wuce ne tsohon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya gabatar da batun samar da dala biliyan ɗaya don gudanar da manyan ayyuka a wani ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi da ya gabatar.
Dillalan man fetur sun ƙara farashin man fetur da aƙalla dala ɗaya kan kowacce lita a duk sassan Najeriya bayan Tinubun ya sanar da cire tallafin man fetur a yayin jawabin da ya gabatar a ranar da aka rantsar da shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Tinubu na neman majalisa ta amince da kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur […]
[…] KU KUMA KARANTA: Tinubu na neman majalisa ta amince da kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur […]
[…] KU KUMA KARANTA: Tinubu na neman majalisa ta amince da kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur […]