Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban ƙasa

0
87
Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban ƙasa

Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban ƙasa

Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na wannan shekarar ba.

Don haka, a wata sanarwa da Bayo Onanuga,
mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman, Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu, wanda ya koma ƙasar a ranar Lahadin da ta gabata bayan tafiyarsa zuwa ƙasashen China da Birtaniya, yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, musamman bayan da aka yi fama da bala’in ambaliyar ruwa.

KU KUMA KARANTA:Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

A taron Majalisar Dinkin Duniya 79, mataimakin shugaban kasa Shettima zai gabatar da bayanin kasa Najeriya ga babban taron, da halartar muhimman abubuwan da suka faru a gefe, da kuma gudanar da tarukan kasashen biyu.

Babban Muhawara mai taken “Kada a bar kowa a baya: Yin aiki tare don ci gaban zaman lafiya, dauwamammen ci gaba da mutunta bil’adama na yanzu da na gaba” zai gudana ne daga ranar Talata 24 ga watan Satumba zuwa ranar Asabar 28 ga watan Satumba. 2024.

Leave a Reply