Tauraron ɗan’adam na farko na Turkiyya da ke sa idanu a duniya ya shafe shekara 1 a sama

0
101

Tauraron ɗan’adam na farko na Turkiyya mai ƙarfin hange sosai da ke sanya idanu a duniya IMECE ya kammala aikinsa na shekara guda a sarararin samaniya, in ji Ministan Masana’antu da Fasahar Ƙere-Ƙere Mehmet Fatih Kacir.

Kacir ya sanar ta shafinsa na X a ranar Litinin cewa IMECE, wanda Cibiyar Bincike Kan Sararin Samaniya ta TUBITAK ta samar tare da harba ta sama a ranar 15 ga Afrilun 2023 ya gudanar da aikinsa cikin nasara.

Ya yi tsokaci da cewa dukkan manyan kayan da aka samar da IMECE na cikin gida ne da suka hada da babbar na’urar daukar hoto wadda ke da ƙarfin gani da iya hasko waje daga nisan kilomita 700.

Kacir ya ƙara da cewa “Tare da ayyukan IMECE a sararin samaniya, Turkiyya ta nuna irin ikon da take da shi a fagen fasahar bincike a sararin samaniya.

“A ranar 8 ga Yulin 2024 za mu harba tauraron ɗan’adam na TURKST 6A kirar Turkiyya a karon farko zuwa sama. Wannan zai sanya Turkiyya shiga jerin kasashen duniya 11 da suka iya samar da tauraron sadarwa nasu na kansu.”

KU KUMA KARANTA: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na MƊD, Guterres, sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

IMECE tauraron ɗan’adam ne da aka samar da kaso 60 na kayan cikin gida Turkkiyya karkashin hukumar TUBITAK.

An samar da ita da dukkan kayan cikin gida, Turkiyya ce ta jagoranci tsara tauraron da fitar da fasalinsa, hada shi waje guda, maƙala masa na’urori, da gwajin aiki da shi.

Tauraron na da ikon ɗaukar hoto da bidiyo a dukkan sassan duniya da na’urarta mai karfin gaske, inda take bayar da bayanai ga ɓangarori masu muhimmanci irin su tsaro da duba muhalli da kula da ibtila’o’i da tsara birane da noma da gandun daji.

Leave a Reply