Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.46 cikin 100 – CBN

0
21
Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.46 cikin 100 - CBN

Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.46 cikin 100 – CBN

Tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kaso 3.46 cikin 100 a zango na 3 na 2024, inda yawan abinda aka fitar ya kai Naira tiriliyan 20.115, daga kaso 3.19 cikin 100 (tiriliyan 18.285) da yake a zango na 2 na 2024, inda galibi ɓangaren da babu ruwansa da man fetur ne ya taka rawa.

Hakan na ƙunshe ne a sabon rahoton tattalin arzikin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar kan zango na 3 na 2024.

A cewar rahoton, an samu sassauci a hauhawar farashi a zangon shekarar, inda ya nuna samun ragowa a farashin kayan abinci daga cikin kunshin kayan masarufin da ake bukata, inda matakin takaita amfani da tsabar kudi ya taka muhimmiyar rawa.

KU KUMA KARANTA: Tallafin wutar lantarki ya ƙaru da kaso 2.76 cikin 100; NERC

Yawan danyen man da Najeriya ke hakowa ya karu, sakamakon inganta tsaro a kewayen bututun man da ke yankin Neja Delta.

Duk da matsalolin da suka ci gaba da bijirowa, CBN ya ce tattalin arzikin ya ci gaba da bunƙasa a zango na 3 na 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here