Tashin hankali ya ɓarke a gabashin Kongo

0
253

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tashin hankali ya ɓarke a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, tsakanin jami’an tsaro da mabiya wata ƙungiyar addini da ke adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya a can.

Rahotanni sun ce sojoji sun kai hari kan wata tashar rediyo da kuma wani wajen bauta a birnin Goma, inda suka kashe mutum aƙalla tara, a yunƙurin hana zanga-zangar ƙin jinin majalisar.

An ce, yayin ɗauki-ba-daɗin, wani ɗan-sanda ma ya rasa ransa.

Har yanzu ana cikin yanayi na ɗar-ɗar a yankin, inda shaguna da harkokin kasuwanci da dama ke rufe.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar ta Kongo na ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya, to amma ana sukan aikinsa saboda gaza kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙungiyoyi masu makamai a gabasin ƙasar.

Leave a Reply